Rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa ta yi nasarar cafke wasu mutane biyu a kan titin Birnin Kudu zuwa Babaldu bisa zargin safarar miyagun makamai daga jihar Filato zuwa jihar Jigawa. Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Alhaji Usman Abubakar Tilli ne ya bayyana haka a lokacin da yake zayyana wa manema labarai yunkurin rundunar wajen tabbatar da samun dorewar zaman lafiya a jihar. Kwamishinan ya ci gaba da cewa, asirin wadannan mutane ya tonu ne a daidai lokacin da jami’an ‘yan sandan ke fatirol a yankin, ta yadda suka tsayar da motar wadannan mutane domin binciken abin da suke dauke da su. Ya ce, bayan an tsayar da wanda ke jan motar ne sai nan take ya tsargu, tare da barin motar ya ruga a guje domin guduwa, amma Allah ya taimaka jami’an tsaron suka cafke shi. Inda Kwamishinan ya ce bayan bincike motar ne, nan take aka sami bindigogi kirar pistol, tare da alburusai a ciki. Haka kuma ya ce, bayan da aka cafke wannan direba, ya bayyana masu cewa, sunansa Ema Gwadal daga jihar Jos, kuma wani mai suna Dembo da ke garin Temper a Karamar Hukumar Kanke na jihar Filato ne ya ba shi domin kai wa wani mai suna Sylbester a Karamar Hukumar Kafin Hausa ta jihar Jigawa. Kwamishinan ya ce, tuni dai suka samu zuwa suka cafke Sylbester da ke Kafin Hausa, tared a yunkurin cafke Dembo, wanda tuni ya ranta a ta kare.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa ta yi
nasarar cafke wasu mutane biyu a kan
titin Birnin Kudu zuwa Babaldu bisa
zargin safarar miyagun makamai daga
jihar Filato zuwa jihar Jigawa.
Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Alhaji
Usman Abubakar Tilli ne ya bayyana haka
a lokacin da yake zayyana wa manema
labarai yunkurin rundunar wajen
tabbatar da samun dorewar zaman lafiya
a jihar.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa, asirin
wadannan mutane ya tonu ne a daidai
lokacin da jami’an ‘yan sandan ke fatirol a
yankin, ta yadda suka tsayar da motar
wadannan mutane domin binciken abin
da suke dauke da su.
Ya ce, bayan an tsayar da wanda ke jan
motar ne sai nan take ya tsargu, tare da
barin motar ya ruga a guje domin
guduwa, amma Allah ya taimaka jami’an
tsaron suka cafke shi. Inda Kwamishinan
ya ce bayan bincike motar ne, nan take
aka sami bindigogi kirar pistol, tare da
alburusai a ciki.
Haka kuma ya ce, bayan da aka cafke
wannan direba, ya bayyana masu cewa,
sunansa Ema Gwadal daga jihar Jos,
kuma wani mai suna Dembo da ke garin
Temper a Karamar Hukumar Kanke na
jihar Filato ne ya ba shi domin kai wa
wani mai suna Sylbester a Karamar
Hukumar Kafin Hausa ta jihar Jigawa.
Kwamishinan ya ce, tuni dai suka samu
zuwa suka cafke Sylbester da ke Kafin
Hausa, tared a yunkurin cafke Dembo,
wanda tuni ya ranta a ta kare.

Comments

Popular Posts