Posts

Sabon Salo: Kansila Ya Nada Masu Ba Shi Shawara

Hassada, Illolin ta da maganin ta!

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa ta yi nasarar cafke wasu mutane biyu a kan titin Birnin Kudu zuwa Babaldu bisa zargin safarar miyagun makamai daga jihar Filato zuwa jihar Jigawa. Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Alhaji Usman Abubakar Tilli ne ya bayyana haka a lokacin da yake zayyana wa manema labarai yunkurin rundunar wajen tabbatar da samun dorewar zaman lafiya a jihar. Kwamishinan ya ci gaba da cewa, asirin wadannan mutane ya tonu ne a daidai lokacin da jami’an ‘yan sandan ke fatirol a yankin, ta yadda suka tsayar da motar wadannan mutane domin binciken abin da suke dauke da su. Ya ce, bayan an tsayar da wanda ke jan motar ne sai nan take ya tsargu, tare da barin motar ya ruga a guje domin guduwa, amma Allah ya taimaka jami’an tsaron suka cafke shi. Inda Kwamishinan ya ce bayan bincike motar ne, nan take aka sami bindigogi kirar pistol, tare da alburusai a ciki. Haka kuma ya ce, bayan da aka cafke wannan direba, ya bayyana masu cewa, sunansa Ema Gwadal daga jihar Jos, kuma wani mai suna Dembo da ke garin Temper a Karamar Hukumar Kanke na jihar Filato ne ya ba shi domin kai wa wani mai suna Sylbester a Karamar Hukumar Kafin Hausa ta jihar Jigawa. Kwamishinan ya ce, tuni dai suka samu zuwa suka cafke Sylbester da ke Kafin Hausa, tared a yunkurin cafke Dembo, wanda tuni ya ranta a ta kare.

152 TASK FORCE BATTALION CLEARS MORE TERRORISTS CAMPS

TROOPS CAPTURE 6 TERRORISTS AT BOBOSHE AND KADAWU

Uneasy calm over killing of 7 Keke riders in Enugu

UK NGO donates borehole to Ilorin Community

4 killed as cult groups clash in Ilorin

RE-TRIBAL WAR AT ARMY BARRACKS 82 DIVISION NIGERIAN ARMY ENUGU THREE SOLDIERS FEARED DEAD

TROOPS CLEAR BOKO HARAM HIDEOUTS IN WULWUTA

RE: ANGRY SOLDIERS BLOCK, RELEASE GOC OVER FOOD, WATER SHORTAGE