Nigeria: Kasuwar Ikom ta kone

Akalla shaguna 40 ne suka kone, a babbar
kasuwar garin Ikom na jihar Cross River
sakamakon gobara a kasuwar, ranar Talata.
Wutar dai wadda ta tashi da misalin karfe 2:00 na
rana, an alkanta ta da matsalar wutar lantarki.
An ce jami'an kwana-kwana ba su iya kai dauki ba
bisa korafin rashin kayan aiki.
Ko a karshen makon da ya gabata, kasuwar Sabon
gari a Kano da babbar kasuwa da ke Birnin Kebbi
na jihar Kebbi sun ci wuta, a inda kuma aka yi
asarar dukiya mai yawa.

Comments

Popular Posts