Ba 'yar mu aka gano ba - Iyayen matan Chibok

Wani mai magana da yawun iyayen
matan Chibok da aka sace, Yakubu
Nkeki, ya shaida wa BBC cewa ba 'yar
su sojojin Najeriya suka ceto ranar
Alhamis ba.
A cewarsa, "Mun bincika sunaye da
hotunan yaran da aka sace, sannan mun
tuntubi dukkan mutanen da aka sace
musu 'ya'ya, amma sun tabbatar mana
cewa yarinyar ba 'yar su ba ce. Bayanan
da muke da su sun tabbatar mana cewa
yarinyar da aka gano ranar Alhamis 'yar
wani Fasto ce aka sace ta daga Madagali a
jihar Adamawa.".
Sai dai da muka tuntubi kakakin rundunar
sojin kasa ta Najeriya, Kanar Sani Usman
Kukasheka, wanda shi ne ya fitar da
sanarwar ceto yarinyar ta biyu, ya
jaddada cewa yarinyar da dakarunsu suka
ceto 'yar Chibok ce.

Comments

Popular Posts