RUGUNTSUMI PART 1... 26/01/2017
Lokaci - lokaci yakan kai kallo ga agogon sa dake
d'aure bisa tsintsiyar hannunsa, fuskar nan tasa sam
babu walwala saboda ya tsani abinda bature ke kira da
(African time).
Yanzu kam ransa ya gama baci, idan kayi la'akari da
yawan tsakin da yake Ja, yau ya tashi da nishadi duk
lokacin da ya tuna yau ne yake cika shekara 28 da
haihuwa, sai ga abokinsa Ahmad yana nema ya bata
masa lokaci wajan zuwa partyn da budurwar sa Teena
ta hada masa.
Sunyi dashi k'arfe bakwai da rabi zai zo ya d'aukesa
amman gashi yanzu ana neman k'arfe takwas harda
rabi na dare, gashi abokansa sun isheshi da kira bama
kamar Teena ba, wacce kusan ko wane minti daya sai
ta kirasa.
Izuwa wannan lokacin ransa yakai matuka wajan baci
kiris kawai yake jira yai bindiga ya fashe.!
Wayarsa yazaro daga cikin aljihunsa yasake gwada
lambar Ahmad sai dai har yanzu ba a daina ce masa
(is not available) ba, bacin ransa yafi na d'azu, a
fusace ya mike tsaye da niyyar yayi tafiyar sa koda
kuwa bisa mashin ne, dama yaso ya hau machine ya
wuce tun dazu sai yayi tunanin ba ajinsa bane a
gansa ya sauko saman machine
Jin karar mota a bayansa yasa shi saurin juyawa,
kicibin idonsa cikin na Ahmad, idonsa a hankali suka
kankance ba tare da saninsa ba, cikin tsananin bacin
rai yake kallon, sam baiyi murna da ganinsa ba, illa ma
wani mugun haushinsa daya kamasa.
Dogon tsaki yaja tare da saurin kauda kansa tamkar
ma bai sanshi ba.
Da sauri Ahmad yafito daga cikin motar yasha
gabansa tare da riko hannunsa gaba daya yana fadin
"Dan Allah Jan kayi hakuri wallahi matsala aka
samu, tun 6:30 na shirya na fito gida nashiga mota,
sai kawai tsoho na yakira ni wai na kaisa gidan
abokinsa Alh Hamza, wallahi dan kawai banida ikon
cewa bazanje bane, shiyasa nayi fuska nakaisa haka
nan"
"Sannan nayi ta k'ok'arin naga na sameka a waya
amman inaaa sam hakan ya faskara, kayi hakuri
abokina nasan ban kyauta ba."
ya fada yana kokarin tallabo habarsa, yana mai
murmushi.
Zuciyarsa ce ta danyi sanyi ba tare da yace komai
ba, ya lumshe idonsa a hankali ya bud'esu, ya juya ya
nufi motar Ahmad, murmushi Ahmad yayi ya rufa
masa baya, Ahmad yaja suka fara tafiya, tare da kure
karar kid'an motar, yana girgiza kai alamar yanajin
d'ad'in yadda kid'an ke fidda sauti.
Yadan karkace kai yakai dubansa ga JAN wanda ke
kallon gefen titi da alama har yanzu bai gama hucewa
ba, ganin hakan ne yasa yafara jansa da hira jefi jefi,
amman sam JAN yayi tamkar badashi yakeyi ba, yaki
tankawa.
Ganin hakan ne yasa Ahmad rage gudun da yakeyi
ya gangara bisa gefen titi yayi parking.
A fusace JAN yace
"Wane irin rainin hankali ne haka? Ya zaka ja ka
tsaya alhalin kasan cewa jiran mu akeyi!?Kai ni idan
kana takama da wannan rubabbiyar motar ne zaka
min wulakanci bari insauka inbar maka abinka!"
Yafara kicin - kicin bud'e Marfin motar, dariya Ahmad
ya kwashe dashi yana fad'in.
"Au! Aini da na dauka kurma na d'auko acikin motar
tawa. Ashe yana magana har ma da fitsara, ya za ai
na maka mutunci na d'aukoka a motata kana wani
daure min fuska, kana kumburi kamar wani fulawa, shi
yasa na faka idan ka sauko daga dokin zuciyar sai
mucigaba da tafiyar! Koya ka gani?"
Ya fada yana ma JAN kallon tak'ama .
Tsaki kawai JAN yayi yakoma yazauna yasaki
kofar.
Ahaka suka k'arasa wajan taron wanda ke shake
tam da yanmata da samari....

Comments
Post a Comment