RUGUNTSUMI PART 6..30/01/2017
Tafiya sukeyi ta takama, duk inda suka gifta sai
an bisu da kallo, bama kamar JAN ba, wanda
idan kaganshi sai ka rantse d’an wani hamshakin
mai arziki ne saboda tsabagen iya daukar
wankansa bayan wankan ne kawai ba aljahu..
Tattaki sukeyi acikin unguwar bawai dan sunsan
inda zasu ba, saran su kenan dama, da zaran
yamma tayi za a dau wanka na fitar hankali,
ashiga zagaye unguwa daga k’arshe ayima
majalisa tsinke, nan za a zauna zaman kashe
wando har zuwa sanda za ai kiran magrib.
Ahmad ne yadubi JAN yana fad’in “wai kai
baba yau naga sai wani shan kamshi kakeyi hala
hajiyar taka bata taboka bane yau??”
Wani irin kallo yayi masa sannan ya dauke
kansa ahankali yayi dan tsaki,
“gabana keta faduwa yau tun safe!” Yakarasa
maganar yana sosa kansa, haka dai gaji da zama
suka mike suka ci gaba da zagaye unguwa shiga
nan fita can daga k’arshe suka yada zango a
dayar majalisar su wanda ke shake da matasa
irinsu, ana ganinsu aka fara ihu irin ta matasa
ana fadin JAN! JAN!! babban yaro! Wani irin
gaisawa suka shiga yi da hannu irin ta matasa
daga k’arshe suka zauna aka shiga hiran,
duniya,
“Wow Kaya!!!!!!!”
Gaba dayan su suka kai dubansu wajan, dan
sunsan me kalmar ta Najib take Nufi
Cikin natsuwa take takunta kanta akasa tamkar
wacce batason taka kasa, doguwa ce sosai, saidai
tanada kira mai kyau, wanda ake kira da Coca-
Cola shape, ta hadu iya haduwa tamkar ita ta
zana kanta, daganin shigar jikinta kasancewa
babbar yarinya ce! Da alama kuma hutu
yazauna ajikinta, kalar fatarta tafi kama data
y’an hutu,
Lokaci daya gaban JAN yayi mugun faduwa
jikake Ras!! Rasss!!!! Ido yakuramata saikace
tsohon makahon daya warke daga makanta,
Azuciyar sa kuwa fadi yake tsarki ya tabbata ga
ubangiji makerin wannan yarinya! Sam yakasa
samun natsuwa jikinsa har wani kyarma kyarma
yakeyi, gaba daya hankalinsa ya dauku akanta,
tuni sauran abokan nasa sundawo haiyacinsu
kallo yakoma kansa, shikuwa ko kifta ido bayayi
dahaka harta bacewa ganinsa tashige wani
lungu, Ajiyar zuciya mai k’arfi yasauke tare da
shafa sumar kansa da hannunsa na dama, dariya
suka kwashe dashi gaba d’ayansu suna fadin
“wannan kayan kalar kace JAN” saidai tuni
hajiya tayi mata fincinkau” acewar Ahmad
wanda ke leka fuskar JAN, harara yasakar masa
yana fad’in
“nace maka ina sonta ne?? Komai ka maida
ni?? Watau gani na mamajo sarkin mata ko??”
Dariya Ahmad yafashe dashi wanda yasa JAN
fusata haryakai masa duka, dariyar dai Ahmad
yacigaba dayi, wani wawan tsaki JAN yayi ya
mike a fusace zai wuce, kirara suka shiga yi
masa wanda yasashi murmusawa dole ya koma
ya zauna,” haba JAN! JAN kud’i, JAN gida , JAN
mota. Na hajiya Kubra bada kanka asare kaje
gida kace ya fad’i.”
Haka dai suka ci gaba dajansa har zuciyar Sa
tayi sanyi, dama shi saurin fushi garesa ga
zuciya naban mamaki.
Najib ne yace kut!!! Amman fa baba Aradu
yarinyar can akwai k’ugu kutumar uba Kai
wannan y’a ta hadu k’arshe…..Ku biyoni Dan cigaba 07066532526

RUGUNTSUMI PART 6..30/01/2017 http://mubarakadamu.blogspot.com/2017/01/ruguntsumi-part-630012017.html
ReplyDelete