RUGUNTSUMI PART 2..27/1/2017

Nan da nan kallo yadawo kan motar su JAN,
kasancewar su kadai ake jira.
Teena ce ta taho cikin wani irin salo mai d'aukar
hankali, tana tafiya gaba daya jikinta rawa yakeyi, har
ta k'araso gaf da motar kafin ta sanya hannu ta bude
murfin motar inda take da tabbacin cewa nan JAN ke
a zaune, gaba daya ta zube a jikinsa, cikin sigar
shagwaba take fadin
"JAN meya tsaida ka harzuwa wannan lokacin ??
Kaduba fa yanda gunnan yacika duk kai daya ake jira
har friends d'ina sun fara mita dan gajiya, wasu har
sun tafi."
Duk wannan maganar tanayin shine da harshan
turanci kasancewar ta yare hausar bai wani zauna a
bakin taba, dago kanta yayi yana kallon cikin idonta
ahankali ya manna mata sumba a goshinta yana fadin
"kinyi k'yau sosai sweetheart" fari tayi da manyan
idanuwanta, tace
"Harma na kaika? sweet JAN"
murmushi yayi wanda yasa kumatunsa lotsawa
alamar dimple, dan yatsanta ta tura acikin ramin tana
wasa a gurin.
"Sweet JAN ina k'aunar wannan dimple d'in naka,"
murmushin yakuma yi yace
" Yanzu dai tsaya nayi miki my sweet Teena.?"
Gilashin motar aka kwankwasa, wanda ya sa suka
dawo hayyacinsu, Ahmad ne wanda tuni yadade da
barin cikin motar, yace
"To jarababbu kufito ku ake jira kun tara jama'a kun
wani kunshe a mota kuna......" Dasauri JAN yatari
numfashinsa da fadin
"To d'an sharri babu abinda mukeyi! Tallafota yayi
suka fito daga cikin motar nanfa DJ yasaki kida, ihu
aka soma yi anayi masu tafi saboda irin haduwar
dasukayi, nan dai aka shiga gudanar da komi yanda
yadace cikin tsari irinta yan boko, kokuma ince irinta
manyan yan bariki wayanda suka san kan duniya,
Anci ansha an cashe son rai ansha an bugu sam
baka iya tantance dan musulmi da akasin hakan acikin
su, hidimace irin ta yayan bariki wayanda suka san
hannunsu, daga k'arshe kowanne yaja hannun
budurwar sa suka kara gaba.
****************
JAN ne kamar kullum yayi wanka ya dauki ado da
ganin sa kaga namijin Duniya, Sai dai ba abin Duniyar,
kwalba ce ba Mai, sabida duk layin su bazaka sami
wanda yakai JAN wanka ba,
a haka ya fito kamar bayason taka kasa.
"Mamasko ni zan fita,"
Yar dattijuwar matar ta kalleshi, cikin fara'a da addu'a
samun sa'a.
Ya fito yana murmushi kai tsaye shagon Abokinsa ya
nufa domin ya sami rancen 1k, Sai dai anyi rashin sa'a
abokin nasa baya nan sai kanin sa, tsaki yaja hadi da
cusa hannun sa cikin sumar kansa da taji mai sai
kyalli takeyi.
Jiki a mace ya fito shagon yayi tsaye yasa hannun
hagun sa ya rike kunkumi yana shafar kansa da dayan
hannun sa,
Wata mota ce Kirar mercedez Ta faka, wata
dattijuwar mata ce ta fito sanye cikin shiga ta alfarma,
Tana tauna chingam a hankali har ta k'araso kusa
dashi, a hankali ya daga kai ya kalli dattijuwar matar,
wanda ya haifar masa da wani mummunan faduwar
gaba, ya rasa gane me yakeji game da ita, lokaci daya
itama dattijuwar ta dago Ido suka hada Ido dashi,
gaba daya kanta ne ya kwance, hakan yasa hatta
tafiya ta kasa yi, ta dabirce har ta matso kusa dashi, a
hankali ya sako mata wani murmushin da ya kara
rudar da ita, ba ita kadai ba hatta shi a rude yake a
lokacin saboda dukkan su sun rasa gane yanayin da
suka samu Kansu a ciki.
Bata bata lokaci ba ta mai magana hadi da tambayar
sa kwatancen wani gida....

Comments

Post a Comment

Popular Posts