RUGUNTSUMI PART 7...31/1/2017
Suna tsakiya da maganar wannan kayan da suka
gani, wayar shi tayi kuka a hankali ya fito da ita
daga aljihunsa, cikin tak’ama da isa ya fara
magana, kasancewar duk dandalin nasu ba mai
waya iPhone 6 sai shi.
Hajiya ce cikin sauti mai d’aukar hankali ya
daga wayar ya fara magana.
Munjiyo muryan Hajiya tana cewa
“Bebena Ina son ganin ka fa, sabida Ina
tsananin kewar ka.”
Wani murmushi yayi, Wanda Saida ya saka ya
rufe ido ya bude su a hankali, duk lokacin da
yake waya da hajiya yana samun kansa cikin
natsuwa da nishadi.
Soyayyar su hadi ne daga Allah bawai sune
suka hada Kansu ba., shakuwar har ta wuce
tunanin mai tunani.
Wannan ne karo na farko da hajiya ta nemi
JAN akan yazo Abuja gurin ta, bayan kokarin da
takeyi na maida shi garin gaba daya.
Baiki tayin nataba, sabida Shima yana son ya
k’ara ganinta ko zai sami peace of mind.
Sun Kare waya akan Saturday zai shigo ya
ganta.
Gaba daya wayar da yayi da hajiya ta mantar
dashi wasu kaya da jabir yake tadin an gani.
Guntun tsaki yayi
” Man ka mana shiru please, wannan fa
karamin kaya ce da zakabi ka rude a kanta”
Ahmad yace,
“Ai dole kace kananan kaya ne tunda kana tare
da manyan kaya.”
Gaba daya dariya suka saka.
Suna mai kirari da na Na hajiya Kubcy.
Shi kuwa sai wani shan kamshi yake yana daga
gira.!
Haka suka Kare sunbatun su, suka watse da
buruka kala kala.
Zaune yake yana chin tuwon da Tsohuwar sa
ta kawo masa, jefi jefi suna hira.
“Yauwa Mamasko, wallahi ina tunanin skull
zasu maidani Abuja da karatu, sabida Ina cikin
students dinda ake alfahari da su a
makarantar.”
Wangale baki tayi sabida kusan duniya ba
abinda uwa takeso gaba ga samun ci gaban
yayan ta.
Babu musu ba komai ta fara masa addu’ar
samun nasara.
Tausayin ta ne ya kama shi, har yaji kamar ma
kada yayi tafiyar, Amma Ina bazai iya barin
hajiya ba, dole yaje yayi tozali da wacce take
sanya shi farin ciki.
Cikin kwarewa ta yaran da suka san kan
duniya yace
“Kinga Mamasko jibi Saturday, zanje na cika
wasu form kila zanyi sati daya a chan mi xan
kawo miki daga Abuja.”
Baki sake Mamasko tace
“Ba matsala Allah ya maka albarka ya kaimu
jibin, ni idan kaje lafiya ka dawo lafiya ya fiye
min komai.”
Nan dai sukaci gaba da hira tsakanin da da
mahaifi….
*** *** *** *** *** *** *** ***
Mamasko sunan da Jalal yake Kiran ta dashi,
Amma sunan ta na asali Hajjo Sa’adatu ne.
Su biyu ne a gurin ta, shi sai yayarsa Jaleelah,
wacce tayi aure tun tuni harda yayan ta kusan 6.
Sun taso cikin rufin asirin Allah, asalinsu Yan
Kano ne, tsangawamar dangin miji yasa Hajjo
Sa’adatu ta bar Kano ta dawo Nasarawa state da
zama, inda anan tayi renon yayan ta Lokacin
Jalal yana da shekara 7 a Duniya, Jaleelah kuma
shekara 8, da gadon mijinta ta data samu ta sayi
gida a nan Nasarawa state ta zauna itada yayan
ta.
Bayan Yan shekaru anan ta sake yin Aure,
Amma mijin sai ya tsangwami yayan nata, tuni
ta kashe auren ta dawo tarbiyar yayan ta, wanda
farin cikin su ya fiye mata komai a duniya.
A hakan tayi ta Sana’ar ta har ta samu karbuwa
a unguwar, kuma tana tafiye tafiye tana siyo
kaya tana badawa sari, akai akai takanje Kano
gun dangin iyayen ta da wannan ta shahara,
kuma duk unguwar an Santa.

RUGUNTSUMI PART 7...31/1/2017 http://mubarakadamu.blogspot.com/2017/01/ruguntsumi-part-73112017.html
ReplyDelete