RUGUNTSUMI PART 3. 28/01/2017

Ya shagala da kallon ta har ta Kare bayanin inda take
nema, Amma kuma shi bai ma ji me take fada ba,
saida ta maimaita masa sannan ya gane Ina ta nufa,
ya gane gidan da take nema Sai dai da Nisa daga nan
zuwa can hakan ya basu damar shiga motar ta dan ya
nuna mata gurin.
Tunani dukan su sukeyi tun bayan shiga motar da
yace mata ta mike wannan hanyar har takai karshen
hanyar yana tunani ,tana tunani,
Dukan su suna jin junan su har cikin Ransu, wani SO
ne da shakuwar junansu sukeji Wanda ya haifar musu
da matsananciyar kasala hadi da dogon tunani,
Dattijuwar ce ta dawo cikin hayyacin ta lokacin da ta
masa wani kallo, Amma Ina shi ya fita zurfafa.
"Bamu kawo bane har yanzu?"
Ta fada tana mai rage gudun motar kadan, a hankali
ya dawo hayyacin sa, ya juyo ya kalleta ya maka mata
wani gigitaccen murmushi, Wanda saura kiris ta saki
kan motar da take sarrafawa cikin gwaninta,
Dauke kansa tayi daga kallon ta a hankali ya furta,
"Mun saki hanyar tun chan baya, sorry ban kula
bane, sai mun dan koma baya kadan."
Ba tare da damuwa ba ta juyar da kan motar ta
koma baya, har suka isa gidan da take nema, bata
bari ya tafi ba saida ta karbi number sa hadi da masa
babbar kyauta, wacce zan iya cewa tunda yake a
Duniyar nan, bai taba rika 50k a hade ba sai yau.
Murna kamar ta kashe shi, ya fito neman 1k Allah ya
bashi 50k daga kwatance.
Gaskiyar magana yafi jin dadin ganin matar akan kudin
da ta bashi, saboda wani jinta yakeyi cikin ransa
Wanda ya rasa gane dalilin hakan, gefen gidan ya
koma ta yanda zai hango ta, har ta Kare abin da take
ta wuce yana labee yana kallon ta.
Hajiya ma ta rasa nutsuwarta tunda ta hadu da
yaron take jin ta rasa sukuni, jiki a mace ta karasa
Abuja.
Wani katafaren gida ta nufa Wanda ko a Maitama
,Shi gida ne na alfarma, Gida ne da ya amsa sunansa
gida,tayi Horn ba bata lokaci aka bude mata ta shiga
cike da tak'ama ta gogaggun mata wayanda suka san
kan duniya,
Wayar ta ce tayi kara, ta duba hadi jan tsaki, har
wayar ta stinke batayi ko gigin daga wayar ba.
Ta fito da key ta bude kofar ta shiga a gajiye saboda
tayi doguwar tafiya, ta fada saman wata sofa dake
gefen palon, wayar ta, ta janyo ta fara Nemo number
Dan saurayin da ya tafi da duk wata nutsuwa tata,
saurayin da ko sunan sa bata sani ba, saurayin da
take jin kamar sun shekara suna tare, ta danna
number sa.
Duk da cewa ya dade yana farautar Kiran ta, hakan
Bai sanya tana Kira yayi gaggawar dauka ba, Sai da
ya dauki lokaci sannan ya daga cikin son jin muryan
wacce yake tsammanin ji.
Itace kuwa, sun gaisa cikin natsuwa da kulawa a
kowane bangare
"Sorry baka gaya min sunan ka ba,"
Murmushi yayi mai sauti, Wanda da ace gaban hajiya
yake da sai tayi suman zaune.
"Sunana *JALAL AMEEN NAZEER* Amma abokai na
suna kirana da *JAN*"
Sunan ya mata dadi, cikin natsuwa ta maimaita
*JALALUDDEN*
Sunyi waya sosai, har take tambayar sa aikin da
yake, ya gaya mata shi student ne, ba tayi gigin gaya
masa abinda ke ranta dangane dashi ba haka Shima
bai fada mata ba, Amma kowa yana jin dayan sa a
ransa.
A haka suka Kare waya cike da kewar junan su,
hajiya cike da shaukin Jalal, yinin ranar ta maimaita
sunan nashi yafi a kirga.
JAN kuwa bai tambayi sunan ta ba, kuma da
gangan yayi haka, saboda ya sami wata dama da zai
kara jin muryan ta, tabbas yana jinta har cikin ransa,
gaba daya ya rasa natsuwar sa yinin ranar,
Baima gane yayi xurfi ba saida dare, lokacin da yazo
bacci anan komai ya chanza, kasa bacci yayi, anan
yayi amfani da damar sa ta dazu ya danna Kiran
wayar ta ba tare da damuwar komai ba.
"Sorry Hajiya na manta ban tambayi sunan ki ba, kiyi
hakuri na kiraki cikin dare kila ma mai gidan yana
kusa,"
Zuciyarsa ce take harbawa lokacin da yace mai gidan
ta, saboda bayason yaji amsa wacce yake tunanin zata
iya tarwatsa masa kwakwalwarsa cikin daren nan idan
yajita.
Daurewa yayi Amma kuma zuciyar sa ta chunkushe,
Daya bangaren kuma Hajiya dariya tayi ta manyan
mata wayanda suka san kan duniya, kasa hakuri yayi
yayi sauri ya katse wayar, cikin mamaki Hajiya ta kara
Kiran sa, amma sai ya sami kansa da kasa daukar
wayar, karshe ma kashe wayar yayi saboda zullumin
amsar da zai samu daga bakin Hajiya......

Comments

  1. RUGUNTSUMI PART 3. 28/01/2017 http://mubarakadamu.blogspot.com/2017/01/ruguntsumi-part-3-28012017.html

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular Posts