EPISODE 3 DANGIN MIJI. 16/02/2016

EPISODE 3 DANGIN MIJI
   Nace Allah sutura wallahi banyi laifi ba, nahau bada hakuri anan nurse din ta ban magani kasan cewar weekend ne ranar kuma ba malamai yasa bawani staff dayasani.muka koma hostel da kyar su furyad suka matsamin naci abinci gashi ranar wai anyiwa ss2 laifi aka taramu a field din makarantan. Aka ware ss1 daban aka bamu purnishment dinmu. Wata sister Y Amina muhammed muna shiri sosai da ita. Tace majidadi kekan aibaki da lafiya jeki daki ki kwanta nan namike na je daki nakwanta kenan har bacci yafara kwasana, kawai naji saukan duka wani irin firgit nayi saida tamin sha biyu 12 a jere, ta daga bulalan ta kundumamin wani ashar meya kawoki hostel, ban iya cewa komai ba sai wani hawaye dayake fitamin nace sister aisha wallahi sister Y Amina ne tace nadawo, tace dakeda Y aminan malapar ubanku!!auxubillah nace dakarfi.
  Wani irin kara tasaka tafara duka na baji bagani saida sandunan suka karye dorinan ya mokade anan metron tashigo ta finciketa ta wurgata gefe. Aisha dama bakida hankali? Me yarinyan tamiki dazaki mata duka har haka? Keda principal gobe Allah yakaimu tafice matron, kuma tajani takaini kan gado, alokacin andawo daga purnishment din bawanda bai tausaya minba, mate dinmu sai zuwa suke suna gaysheni nayi narau narau ko ina a kumbure, wani irin zazzabi yarufeni haka narinka jinya har ran monday. Dayake English mukedashi first period Ahmed G nashigowa yalura bananan a zatonsa ko lattin dana sabayine, anma dayaga yagama first period baiganniba. Yace wasu zafyra ina Mayah? dama Mayah yake cemin sukayi narai narai da ido sai yan ajin sukace batada lafiya. Meya sameta? Anan kowa yayi tsit kowa na tsoron fada daga baya azo aci kaniyanshi. Ya buga musu tsawa badaku nakeba? sai furyad tace sister head girl ne tamata duka. Wani irin razana yayi what!!? metayi? sukayi tsit nanma. Yace furyad tatashi tadaukoni takaini dispensary shikuma yaje gun, anan nurse din tabashi labari meya faru. Yaharzuka sosai tunda take dashi bata taba ganin bacin ransaba, adaidai nan muka shigo yana ganina yace ashhaaa. Nurse shine ba’a mata treatment ba! Zafyra tace a a. Tamata wani dukan aka karayi.yace kuzauna anan amata duk abinda yadace. Yakallen yayi murmushin dole wanda nasan a dole yayi sannu mayah.
 Allah yakara sauki yafice bayan angama wankemun ciwukan ina zaune kawai naga kaf ss2 wanda suka min duka dawanda suka sa baki dawanda suka sa hannu sunyi layi a kofan dispensary, yaleko mayah fitonan. Na fita ina kishingide gatanan kufara. Abun yadauremin kai daya bayan daya suka taso sunaban hakuri, nayi shiru a zuciyata nace don Allah ahmed G karufamin asiri kar nakoma hostel suci kaniya na. Ina wannan tunanin saiga aisha alkali itama tazota taban hakuri, sannan tajuya wani fincika yamata ya gaggaura mata mari. Dan ubanki haka mukayi dake? Alkawarin damukayi dake kenan? Zaki zaga kici amana? dama haka kike? to a kunnen umma. Wani irin kuka tasaka haba big bross kayi hakuri mana abun yadaure min kai matuka, dama akwai alaka tsakanin aisha alka da ahmed G?
Yasa sukayi layi tundaga admin block yake sasu tsallen kwado har dinning hall. Yana binsu da bulala, sunyi narai narai kam balaifi duk malamin dayazo yamishi magana baya ko kallonsu don haka sai su juya batare da sunce komai ba. Bayan sungama tsallen kwadon. Yace yau anhutar damasu aikin makaranta. Haka yasa suka share classes, hostel, da kuma admin block. Yasa suka wanke bayan gidan teachers ranar har karfe biyar suka kai suna aiki nikuwa yafita yakawo abinci ya kawo mana mukaci mukayi nak hankalina a kwance.furyad kuwa duk tabi ta tsure wai kar a koma hostel sumana duka. Makaranta kuwa kowa sai ya tabbatar da zarginsa akan cewa muna soyayya da ahmed g inbahaka ba wannan hukunci ai tsauri gareta. Bayan yagama sasu aikin yakirani sannan yace gata agabanku barin rantse muku kuji, wallahi tallahi ko dauko cokali kuka sata zaku wahala ahannuna. Inada sunayenku ba ita zata fada munba, securities nasaka donhaka saiku kiyaye. Sannan dukka masu post a cikin ku, daga yau ku tabbata kunyi ban kwana dashi zansa principal gobe ya cireku. Ku bacemun. kowaccensu cikin sanyin jiki suka mike, aisha alka ce tazauna. yace tazo tataho tare da durkusawa, yaya kayi hakuri bazan karaba.




Zaku iya karanta dukkan labarin nan, dan haka kudanna wannan shafin, Mubarakadamu.blogspot.com.... Dangin Mijina Episode 3 February 14 2016 http://Mubarakadamu.blogspot.com/2016/02/dangin-mijina-episode-3-february-14-2016.html?spref=tw

Comments

Popular Posts