RAHOTO: Hatsabibiyar Dodanniya Ta Bulla Da Shan Jini A Gashua

Wasu bayanai da LEADERSHIP Hausa ta
samu daga jama’a da dama a Unguwanni
daban-daban da ke garin Gashuwa ta
jihar Yobe, sun nuna cewa jama’a suna ci
gaba da fargaba dangane da yadda wata
halitta mai kama da Dodanniya ke shiga
gidajen jama’a tana yin awon gaba da
dabbobinsu, wanda daga bisani sai a
tarar an kwashe kayan cikin dabbar an
bar gangar jikin, a wani lokaci kuma sai a
tarar da dabbar kwance an tsotse jininta.
Bayanan suka nuna cewa, wannan
babban abin al’ajabi yana ci gaba da
daure wa jama’a da dama kai, bisa yadda
matsalar ke ci gaba da yi masu barazanar
da ta kai wasu ba sa samun runtsawa,
yayin da wasu ke sintiri don tsaron
unguwannin nasu har gari ya waye.
Wani mazaunin wannan wuri, Malam
Muhammed Abbas (Malam Awan) ya
bayyana cewa, “hakika wannan al’amarin
ya daure mana kai. Saboda ranar Jumu’ar
da ta gabata, wannan Dodanniyar ta
shiga gidan makwabcina ta kama tunkiya,
inda ta kwashe kayan cikinta, ta bar
gangar jikin a kofar gida. Kashe gari kuma
ya sake dawowa, to shi ne sai muka
fahimci abin ba na zama ba ne, sai muka
fara tunanin kada fa wannan abin ya
tsallaka zuwa ga ‘ya’yanmu.”
Ya ci gaba da cewa, “hakan ta sa muka yi
shawarar cewa ba mu ga ta zama ba,inda
muka nemi matasan Unguwa majiya karfi
muka rarraba su kashi-kashi a cikin
Unguwar, wasu a kan itace, kuma
kowanne rike da sanduna da fitilar
hannu; can cikin salasainin dare sai muka
gansu sun tunkaro mu su biyu, shi ne
daya daga cikinmu ya dalla masu hasken
fitila, cikin tsoro sai suka fita a guje, muka
bi su,mutane sun tasamma dari, daya
daga cikin Dodannin, wajen shan kwana
sai da ya yi karo da katanga, kamar ya
fadi, a haka ya shanye kwanar. Kuma
abin mamaki, hatta karnuka da suka
gansu, fadawa cikin gida suka yi, kuma
kafafunsu hudu ne kamar dangin kura,
kuma kamar mutum daga gaba, sannan
babu jela, amma da muka rutsa shi sai ya
bata bat.”
Malamin ya kara da bayyana cewa,suna
cikin matukar fargabar wannan al’amarin,
inda ya ce, “kasancewar yadda wannan
abu ke mana ta’adi, musamman yadda
ba ya kama ramammen rago ko tinkiya,
sai kosasshe, kuma ba ya cin akuya,
yanzu haka wasu sun sayar da dabbobin
su. Sannan yanzu mun yi shawarar mu
hadu mu gaya wa Sarkin Bade halin da
ake ciki. Sannan za mu shaida wa jami’an
tsaron ’yan sanda da sojoji don gudun
kada matsalar ta wuce inda take yanzu.
Amma gaskiya muna fuskantar damuwa.”
Ita kuma Malama Jimmala, wacce
wannan abu ya sungume mata tinkiya,
sannan ya wawushe kayan cikinta ya jefar
da ita a kofar gida, ta bayyana cewa, “da
misalin karfe biyu muna daki sai muka ji
motsi a waje, dayake mun dan tsorata, ba
mu fito ba, shiru har gari ya waye, shi ne
sai muka ga babu tinkiyarmu, mun dauka
ko barawo ne, abin mamaki sai muka
ganta a kofar gida a mace bayan an
kwashe kayan cikinta. Sannan wani abin
mamaki, babu wata alamar jini ya zuba.”
Bisa ga bayanan da wakilinmu ya tattaro
a garin, sun bayyana cewa wannan Dodo
ya karade Unguwanni da dama, tare da
hallaka dabbobi masu yawa, sannan
kuma duk wani abu da jama’a ke yi ta
hanyar yi masa a-tare, abin ya faskara.
Saboda wani lokaci sai an yi masa kofar
rago, amma sai ya sulale a rasa inda ya
shiga.
Amma dai wasu da suka sha yin
arangama da ita sun ce, wani lokaci ta
kan zo a siffar mutum, wani zubin kuma

Comments

Popular Posts