Musayar Kalamai Game Da Ci Gaban Shugabancin Bukola Saraki

Kiran da wasu yan Majalisar Dattawa
sukayi ga shugaban Majalisar Bukola
Saraki, domin ya sauka bayan fuskantar
zargin rashin bayyana kaddarorinsa ga
kotun da’ar ma’aikata, ya sanya dan
majalisa dake matukar mara masa baya
maida martani.
Tuni ma dai shugaban
kwamitin labarun majalisar Sanata Aliyu Sabi,
yace ba ayi kiran bisa manufa mai kyau ba ne, in
za a tuna kotun koli ta ‘ki amincewa da bukatar
Sanata Bukola kan hana kotun da’ar ma’aikata ci
gaba da yi masa bincike kan mulkin sa tun yana
gwamnan jihar Kwara.
Masu tunanin ko Saraki na dagewa kan zama a
kujerar shugaban Dattawa ne don ya kara karfi
don ya nemi shugabancin Najeriya a shekara ta
2019, wannan batu ba gaskiya bane, inji
mukarrabin Sarakin Sanata Isa Hamma Misau,
har ma yace su shugaba Buhari suke marawa
baya.
Mukaddashin shugaban kwamitin amintattun
PDP Sanata Wali Jibrin, yace zasu tsayar da dan
takarar su daga Arewa a shekara ta 2019, don
fuskantar APC. Yana mai nuna farin jinin PDP
ma ya fara dawowa.
Duk da dai riga mallam masallaci ne batun zaben
2019, ga masu niyyar takara ko marawa wani
baya amma tuni siyasar Najeriya ta fara tafiya da
batun wannan zaben. Zuwa yanzu dai shugaba
Buhari na dagewa ne kan yaki da wadanda ake
zargi sun karkatar da kudin sayen makamai fiye
da dala miliyan dubu biyu, kuma babu alamun
yana nuna alamar neman zarcewa.

Comments

Popular Posts