Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Yankin Damfar Wanda Yayi Sanadiyar Rayuka
Wannan na zuwa ne
yayin da gwamnatin jihar ke kokarin kiran
wannan babban taro na masu ruwa da tsaki, don
lalubo hanyar magance tashe tashen hankula
dake da nasaba da fadan kabilanci.
A cewar wasu shedun gani da Ido wasu
maharan dauke da makamai suka yi dirar mikiya
a yankin Sarkin Noma dake gundumar Damfar
na karamar hukumar Ibi a Kudancin jihar
Taraba. Ina aka sami asarar rayuka ciki ma harda
mace da kuma kananan yara.
Shi dai yankin Ibi na daga cikin yankunan dake
fama da tashe tashen hankula a jihar Taraba, da
sautari kan yi nasaba da fadan kabilanci ko na
addini. Sai dai wasu da abin ya shafa sunce
maharan sun kai hari inda suka kashe mutane 6
mace da ‘ya ‘yan ta da mijin ta suka kuma
konesu kurmus.
Yanzu haka dai rundunar yan sandan jihar
Taraba ta tura karin jami’anta kamar yadda
kakakin rundunar ya shaidawa wakilin Muryar
Amurka ta wayar talho, don a gudanar da
bincike don gano wandanda ke da hannu a
wannan lamari, kuma wannan mako na zuwa ne
yayinda gwamnan jihar Darius Dickson Ishaku,
ke gabatar da wani taro na samun zaman lafiya a
jihar.

Comments
Post a Comment