♥♥♥AURE KO ZAMAN GIDA♥♥♥°°°°°°°° °°° °PART 4°°°°°°°°°


…Iya tunanina aurena da wani dan
mashukurin mai
kudi rana daya akayi shi dan jama'ar da
suka taru
sunfi qarfin suzo aurena amma daga
qarshe
mungane gurin auren nawa sukazo,Har
bayan
daurin aurena ina gidanmuban tareba,
Bana fita ko
ina, Sai taya maman jamila aiki, Ke in
gayamaki jabo
wllhy saida nayi shekara biyar agidanmu
ba miji ba
labarinsa kuma ba zancen tarewa, Har na
balaga,
Ba miji inason inyi magana amma kunya
ta hanani
yin magana duk qannena mata jamila da
hafsatu an
musu aure jamila da wani har ta haihu da
wani ciki
ajikinta hafsatu kuma da cikinta tsoho,
Nigani agida
farko abin baya damuna kuma sam ban
fuskantar
tsangwama agurin maman jamila, Yanzu
na girma
nasan miye aure saboda ina zuwa wata
islamiya
dadare ta matan aure a unguwarmu,
Inajin
abubuwan da ake koya mana mata da
wuri suke
zuwa dan suyi ta tadi, Mijina kaza mijina
kaza nidai
bana ce musu komai, Abin duniya ya
isheni nayanke
shawarar zan yiwa baba magana sai dai
kuma
kunya nakeji nace ko infara yiwa maman
jamila
maganane inji abinda zatace, Haka kuwa
akayi, Ina
biya mata karatun qur'ani bayan munqare
muna hira
saina cemata wai maman jamila waye
mijina..? Naji
kamar bata jini ba namaimata tambayar,
Ta d'ago
ido ta kalleni tace mun kitambayi babanki,
Nayi shiru,
Ban qara cewa komaiba, Munqare karatu
da ita na
shige daki, Sai tunani kala kala nakeyi
gaskiya
inason sanin miye matsayina matar aure
ko
bazawara? Zaman aure nake ko zaman
gida?
Shekara biyar ba miji ba labarinsa sai wani
niqab da
baba yasani sakawa tunda aka dauramin
aure, Yan
kwanakinnan nashiga damuwa sosai sai
nake
tunanin ko dan banida uwane aka yimin
haka, Lallai
maraici hadarine, Nashiga rera kuka mara
sauti nayi
wata biyu Kullum sai nayi kuka duk wata
walwala ta
gushe mini banida aiki sai tunani da
damuwa nashiga
tsaka mai wuya narame, Na kode, Nayi
baqi, Duk
wata halitta ta jikina saida ta chanza.. Na
yi alwashin
zanyiwa babana magana, Bayan yadawo
daga
kasuwa nace inada magana dashi yace to
naje
gurinsa, Inson inyi magana sai muryata ta
fara rawa
bansan lokacinda kuka ya subucemin ba
nayi kuka
sosai baba ya rasa gane kaina gashi ba
kowa
agidan saini nima dan banje islamiya
bane, Daqyar
nasamu nayi shiru amma nakasa
tambayarsa, Can
baba yace nasan zaki damu ace shekara
biyar da
watanni da daura miki aure amma
bakisan mijinkiba.!
kuma baki tare Gidankiba ba ,Amma kiyi
haquri
nasan banmiki adalciba, Nafarko ban baki
damar
zabar mijin da ranki yakesoba ban
tambayi
ra'ayinkiba inji shin kina sonsa ko yaya,!
Bakisan
wayeba bakisan komai akansaba hasalima
bakisan
wayeshiba ban barki kinyi karatun
bokoba, Sannan
shekara biyar dai dai da rana daya
bakimin magana
ba Allah yayi miki albarka kuma mijinki
wannan
shekarar zai dawo insha Allah, Idan ya
dawo tare
gidanki tashi kije ki kwanta Allah yayi miki
albarka,
Koba komai raina yayi sanyi najin cewa
mijina zai
dawo wannan shekaran dan wllhy na gaji
da zama
da igiyar aure akaina…
Kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN
GIDA part 5

Comments

Popular Posts