Nigeria da China Sun Kulla Muhimman Yarjeniyoyi Shida

Nigeria za ta shigar da kudaden kasar
China cikin kudaden ta na asusun waje,
a ci gaba da tabbatar da dorewar
zumunci tsakanin ta da kasar China.
A nahiyar Africa, Nigeria za ta kasance
kasa ta farko da ta shigar da kudaden
kasar China cikin kudaden da take dasu a
waje.
Wannan na daga cikin yarjeniyoyi shida da
Shugaban China Xi Jinping da Shugaban
Nigeria Muhammadu Buhari suka sanya
hannu ciki, a birnin Beijing.
Shugabannin biyu sun sanya hannu cikin
yarjejeniya da suka hada da harkokin
masana’antu, sufurin jiragen sama da
harkokin samar da muhimman bukatu
na jama’a.

Comments

Popular Posts