Nigeria: 'Kowa sai ya biya haraji a Kaduna'

A Najeriya, gwamnatin jihar Kaduna ta bullo da
wata sabuwar hanya ta karbar haraji mai suna
'presumptive Tax'.
Gwamnatin jahar ta ce ta bullo da tsarin ne
domin karbar haraji a hannun masu kananan
sana'o'i,wadanda a baya ba sa biyan haraji.
Shugaban hukumar tattara kudin shiga ta jahar
Alh Muktar Ahmed ya shaida wa BBC cewa
gwamnatin ta yi haka ne a kokarin da ta ke yi na
kara hanyoyin samun kudin shiga a jahar.Raguwar kudaden dake zuwa jahar daga aljihun
gwamnatin tarayya ce ta sanya jahar Kaduna
neman hanyoyin samun kudin shiga don yin
ayyuka ga jama'a.

Comments

Popular Posts