Sabon Salo: Kansila Ya Nada Masu Ba Shi Shawara

Wani Kansila a jihar Kano, Hon. Kabiru
Shugaba, Kansila mai wakiltar Mazabar
Unguwar Kwanar Diso da Lungun Makera,
ya nada masu ba shi shawara har mutum
goma sha biyu. An gudanar da taron
nadin ne a harabar Karamar Hukumar
Gwale a makon da ya gabata. Hon.
Kabiru, yana daya daga cikin Kansiloli 10
da ke Karamar Hukumar Gwale, wanda
kuma ake ganin nan ne cibiyar siyasar
Kano a tarihi, da kuma dangantakar
Malam Aminu Kano da Karamar Hukumar
Gwale.
Wadanda Hon. Kabiru ya nada, sun hada
da Sunusi Alhaji Jibrin, wanda zai bas hi
shawara kan harkar ilimin matasa, Malam
Abdulkarim Limamin Masallacin Juma’a,
harkar addini, Alhaji Liman kuma zai bas
hi shawara kan harkar noma. Sannan
akwai Alhaji Sa’idu Kura, mai bad a
shawara kan harkar siyasa, Alhaji Namadi
kuma kan ayyuka na musamman, Alhaji
Murtala Ado Kwage, harkar matasa 1,
Alhaji Tijjani Harkar matasa na II, Malam
Ali Mai ba da shawara kan harkar
dattawan Unguwa.
Sauran sun hada da Malama Zainab mai
ba da shawara kan Harkar zawarawa da
’yan Mata. Sai kuma Malama Halima mai
bad a shawara kan harkar matan aure,
yayin da Malam Mai Citta ya zama mai
bad a shawara kan Harkar siyasar
dattawa, Malam Alhaji kuma ya samu
matsayin mai ba da shawara a ofisshin
Hon. Kabiru.
Wannan taron rantsuwar ya samu
halartar al’ummar Karamar Hukumar
Gwale da kewaye, inda Hon. Kabiru ya
bayyana cewa ya nada kowane daga
cikinsu ne bisa chanchanta da kuma irin
gudumuwar da suke bayarwa gareshi tun
kafin ya nada su

Comments

Popular Posts