Hassada, Illolin ta da maganin ta!

1) Hassada shine mutum yaji zafin wata ni'ima da
Allah yayiwa wani bawan sa, koda baiyi fatar
gushewar ni'omar ba. [Ibn Taymiyya da wasu
malamai]
2) Hassada halin yahudawa ce [ Qur'an 2: 109,
4:54, 48:15]
3) Hassada tana kama wanda akayiwa ita, komai
imanin sa; ta kama Annabi Yusuf (A.S), kuma Allah
ya umurci Annabi (S.A.W) daya nemi tasri daga
sharrin mai hassada [Qur'an 113:5].
4) Karanta azkar na safe da yamma, da karanta
Fatiha, da karshen suratul Bakara, da ayatul
Kursiy da suratul Falaq da Nas ya na kariya da ga
hassada da bala'oi [hadissai da yawa]
5) Boye ni'ima ga wadan da ka ke tsammanin
zasuyi ma hassada yana kareka daga hasada ya
yardar Allah [quran 12:5].
6) Annabi (S.A.W.) yahana hasada, cikin hadissai
dayawa cikin su akwai [ Muslim 2559]
7) Mai hassada yana fada ne da Allah, domin Allah
shi yake yin ni'ima ga wanda yaga dama, kuma
Allah shiyafi sanin wanda ya cancanta. [Malamai]
8) Mai hassada kullum yana cikin bakin ciki da
bacin rai wanda ba lada akai [ laa tahzan, A'ed
alQarny]
9) Hadisin da ya shahara na "Hasada tana cin
ayyukkan..." bai inganta ba.
10) Allah yayi mana tsari daga hassada, yasa kada
muyiwa wani, kuma ya tsre mu daga masu yi
mana.

Comments

Popular Posts