RUGUNTSUMI THE END

Ba Wanda yayi ta kan Hajiya, illa gun Mamasko
da aka nufa ana son ta far fado, Hany kuwa gaba
daya bata iya ko daga kafa, ga cikin nan da ya
mata mahaukacin nauyi, duba ta kai gun
mahaifiyarta da taga gaba daya ta kara fita
hayyacinta, Sai wani surutai takeyi Wanda ba ta
gane mi take fada, takai duba da jinjirar da ke
kwance tana sharar bacci, kaninta Kuma dan
mijinta, zuciyar tane ta rufe ta daina gani gaba
daya. ta rasa mi takeji, bakin ciki ko nadama,
tabbas rayuwarta cike take da bakin ciki, ta rasa
gatan uwa, ta tashi gun dangin uba dan gudun
gurbacewar tarbiya, Amma Kuma Sai ya zama
bata sami kulawa ta musamman a gun wayanda
suke takama da sune iyayen taba, har takai ta
auri mijin mahaifiyarta.
Ta tuna lokacin da Jan yazo da zancen
aurenta, k’anin baban su bai tsaya binciken
komai akai ba, kawai yace ya turo magabantansa
tamkar sun gaji da ita aka aurar da ita ba
bincike ba komai, wannan yasa auren su bai dau
lokaci ba.
Hayaniyar ce ta karu a gun, wanda yasa
hankali ta ya dawo jikinta, ta dawo dogon
tunanin da takeyi.
Mahaifiyarta ce take wasu surutai.
Tamkar wata zararra haka Hajiya ta dinga
fadin
“Mekuke nufi?”
kada dai kuna nufin Jan d’an wannan matar
ne?” wayyo nashiga uku na lalace ni Kubra ?”
wani irin ihu tasaki tamkar ba itace akaima aiki
ba, da sauri Hannatu ta riketa duk kuwa da
tsananin haushinta da takeji, ganin zata fado
daga gadon tana sambatu.
Ruwa Jan ya shafa ma Mamasko a fuska, tasaki
wani irin ajiyar zuciya a hankali idanuwanta
suka shiga budewa, kuka tafashe dashi tana
kokarin tashi tsaye, Jan ne ya kamata ta mike
tana nuna Hajiya Kubra wacce ke kuka tamkar
ranta zai fita.
Wani irin mugun kallo mai wuyar fassarawa
Mamasko tashiga aikawa Hajiya Kubra dashi tana
nunata da dan yatsa, murmushin takaici
Mamasko tayi tashiga fadin
“Malamar islamiya kenan! Ai shi Allah ba
azzalumin bawan sa bane sai wanda ya zalunci
kansa! Da dukkan alamu kinyi amanki ne kika
lashe! Dan abinda idanuwana suka gane min,
kunnuwana suka jiye min gangar jikina ya bani
hankalina da tunanina suka raya min shine Jalal
kika Aura! Bayan kingama watsewa dashi, lallai
wannan ishara ce Allah ya fara nuna maki tun
anan duniya! Lallai ko baccin mutuwa nayi na
farka bazan mance wannan mummunar fuska
taki ba.”
Ta gyara tsayuwarta ta koma fuskantar Hajiya
Kubra wacce ke ta raba ido tana kuka, rike da
zuciyar ta wanda kemata barazanar tarwatsewa,
ta nuna Jan da dan yatsanta,
“kinga wannan dan dake tsaye? shine wannan
tatsitsin jaririn wanda ki ka haifesa daga karshe
kika dire min shi kika gudu kika barni dashi
cikin qishirwa mai tsanani.! Wanda tun daga
ranar ban kara sakaki a cikin idanuwana ba sai
yau da Allah yatoni asirinki, kikai Amanki kika
lashe dakanki saboda tsabagen son zuciya irin
naki!”
“Zaki iya tuna ranar Assabar da muka hadu
dake a kasuwa??
Kina sanye da babban Hijabi?, Kika ce mun ke
malamar islamiya ce, kina bani rikon jinjirin
nan” ta nuna Jan da yatsa, “Wanda Na tambayeki
sunan sa, kikace mun Muhammad? Nace bashida
lakabi kikace mun kina zuwa?
Sabida tsakanin kukan da yakeyi, dan kishin da
yakeji, kikace bari ki karbo masa ruwa?
Tin daga ranar ban kara ganin ki ba, kin tuna
ranar?”
 Murmushin takaici Mamasko ta kara Saki, akaro
na karshe tace to malamar islamiya, wannan yar
dakika haifa da danki na cikin ki ” *Y’A CE KO
JIKA?*”
takuma juyawa ta nuna cikin dake jikin
Hannatu tace shi kuma wannan na ciki dabai zo
duniya ba ” *D’AN KISHIYA NE KO JIKA?*”
Gaba daya dakin yayi tsit bakajin komi sai sautin
kukan Hajiya dake tashi,
Tabbas ta tuna lokacin da ta gudu daga sayen
ruwa ta baiwa Mamasko rikon jinjirinta ta gudu
ta barshi yana tsalla ihu.
Jinjirin da shine cikin shegen ta na farko tun
kamin tayi Aure,
Lokacin da tayi cikin duk wani abin zubar da ciki
tasha amma cikin yaki zubewa, iyayen ta sun
ringumi kaddara har ta haifi cikin amma ita ta
kasa rungumar kaddara inda tayi alwashin sai ta
salwantar da da jinjirin ta ko wace irin hanya,
sabida ba zata bari mijin da zata Aura ya gane
cewa ita ba budurwa bace.
Wannan dalilin yasa ta barwa Mamasko rikonsa
tayi amfani da damar siyo ruwa ta gudu ta bar
mata shi.
Wata gumza ta saki, mai kama da kakarin
mutuwa.
A gurin kowannan su na cike da tsananin
mamaki da Al’ajabi na wannan lamari dake
faruwa, Jan wanda ke tsaye tamkar an dasa shi,
kwakwalwarsa nata hautsinawa, yama rasa
awace duniyar yake ciki Jikinsa sai rawa yakeyi
zuciyar sa na zaiyano masa kalaman Mamasko.
“wai me wannan yar tsohuwar take nufi ne?
Tana nufin shi Jalal ya auri uwarsa data haifeshi
da cikinta bayan ya gama lalata da ita daga
karshe yai mata ciki harta haifa masa y’a?” Ya
kuma auri kanwar sa wacce suke uwa daya har
yayi mata ciki haihuwa yau ko gobe?”
” No!!!!!!!!!!!!”
Yafada dawani irin karfi ya dunkule hannuwa
tamkar mai shirin danbe, wanda ya jawo
hankalin likitoci zuwa dakin, lokaci daya yafara
wata irin dariya yana zubar da hawaye, yana
fadin “No! No!! No!!! Ba ita bace!!!” Sai Kuma
yasaki wata dariyar mai karfi yana fadin
“yes! Yes!!”
Sai yau ya gane son da yake ma Hajiya son d’a
da mahaifine.!! Ya gane tausayin ta da yakeji
tausayin da gun uwarsa ne, tabbas son uwa gun
danta daban yake, sau da dama ya kan rasa
wane irin
yakeji game da Hajiya, Hannah ma haka yakeji
game da ita, itama Hajiya tana jin hakan , Hany
ma takan ji haka, Sai suka tafi akan cewa
soyayya ce daga Allah.
Gadan-gadan yayi kan Hajiya ya shaketa yana
dariya, hawaye na sauka a saman kumatunsa,
yana fadin
“No! No! Ba ita ce Mamata ba Yes! Yes!
Mamasko tace kece Mamata” Yana jijjigata iya
karfinsa yana wannan sunbatun,
Duk Wanda ya kallesa yasan ya sami tabuwar
hankali, Da kyar likitocin da kawu sukai nasarar
banbaresa ajikin uwar sa Hajiya Kubra.
Wani irin ihu yayi hade da zabura ya watsar
dasu ya fice da gudu.
Da gudu daya daga cikin likitocin ya rufa masa
baya tare da yi ma masu gadi izinin rufe Gate
din asibitin Amman ina tuni Jan ya arce a dari,
da kyar suka kamo shi suka masa allurar bacci
sannan ya yiyi bacci.
Hannatu kuwa lokacin da ta fahimci mijinta
yayan tane, bayan sunun mijinta ya auri uwarta,
Ashe shima uwarsa ce, cikin ta ya fara
murdawa, ta durkushe tana murkususu da
alamar nakuda ne yakama ta babu wanda ya
lura da ita sai dawowar dayan likitan cikin dakin
shine ya kula da halin datake ciki, nan danan
aka nufi dakin haihuwa da ita abin gwanin ban
tausayi.
Da sauri likitan da yayi saura a cikin dakin ya
karasa gun Hajiya wacce ke wani irin kakari rike
da zuciyar ta, gaba daya kuka mutanan cikin
dakin keyi babu mai lallashin wani kawu ne
kawai mai karfin halin dayake ta tausar zuciyar
sa, batare da zuciyar sa tayi rauni ba.
Likitan ne ya umurcesu da su basu waje zai
duba Hajiya wacce tuni tafice a hayyacin ta.
BAYAN AWA UKU
Likitan dake kula da Hajiya ya fito fuskar sa cike
da gumi, da sauri suka nufosa da kyar ya iya
bude bakinsa yace kuyi hakuri tashiga COMA
Amman in sha Allahu nan da kwana bakwai zata
farfado, daga haka bai kara cewa komi ba yayi
gaba abinsa.
Likitan dake kula da Hannah shima yafito ya
sanar dasu Allah ya sauke ta lafiya ta sami da
namiji, itama mai jegon tana lafiya lau.
Ajiyar zuciya suka saki gaba dayan su zuciyar
kowanne na raya masa wani abu daban.
Jaririyar da Hajiya ta haifa aka miko masu,
Mamasko tasaka hannu biyu da karbeta zuciyar
ta na harbawa, ta tsurawa diyar ido tana kallon
ikon Allah gaba daya diyar kama take da Jan
tamkar kwabo da kwabo. Likita ne ya fito da
jinjirin da Hany ta haifa, Mamasko cikin kuka
tasa hannu ta karbesa, Shima kamar su daya da
Jan, Kuka take kamar ranta zai fita, tayi burin
Jalal ya hadu da mahaifiyarsa Amma ba ta
wannan mummunar hanya ba.
Kallon yaran take tana hawaye su Kuma Sai
bacci suke abinsu, su Kam an cutar dasu basu
san hawa ba basu san sauka ba.!!!
BAYAN KWANA HUDU.
Tuni an sallami Hannatu, kakarta ta matsa
lallai sai dai su koma dan ta kula da jikarta, dan
gaba daya bata cikin haiyyacinta tayi wani
zurum, Kuma taki baiwa jinjirin Nono ko
karbansa ta kasa yi, idan ta tuna cewa ta kwana
da yayanta Sai taji tamkar Allah dauki ranta dai-
dai wannan lokacin, wace irin jarabawa ce Allah
ya mata? Ko wane lokaci tunanin da take yi Sai
ta fashe da  kuka, bayan Wannan ba abinda take
yi, duk ta lalace ta koma tamkar gawa, haka
suka wuce kowanne ransa babu dadi.
Mamasko ce ta tsaya da Hajiya saboda tausayin
jaririyar da Allah ya aza mata, wacece take kallo
a matsayin yar jikanta, ga uba chan har yanzu
bai dawo hayyacinsaba.
BAYAN KWANA TARA.
A yaune Hajiya Kubra ta farka, sai dai batayi ko
minti goma ba Allah yayi mata rasuwa
kasancewar zuciyar ta tariga ta buga.
Allahu Akbar.!!
Likitoci sunyi kokarin daidaita hankalin Jan Sai
dai abin yaci tura, ya riga ya rasa hankalinsa
gaba daya, zuciyar sa ta kasa tariyo masa yanda
ya kwanta da mahaifiyarsa da Kuma kanwars
har dukan su suka haihu, ya kasa iya wannan
tunanin, daya fara Sai kawai komai ya tsaya
masa, Sai ya fara dariya, yana zubar da hawaye,
yana jin ya za’a yi ma hakan ta kasance, sai
yana kallon abin a matsayin abin da bazai taba
yiwuba ba, wannan dalilin yasa ya kasa samun
hankalin sa.!
Hannatu ce ta karbi diyar Hajiya Kubra bayan
komi ya lafa tacigaba da rikon ta, tayi bakin
cikin mutuwar mahaifiyarta, dukda cewa ta tsani
halayyar ta Amma tana kaunar uwarta, duk
lokacin da ta kalli Jinjirar wacece aka saka ma
suna Zainab Sai taji tausayin ta, idan ta girma
ya zata rayu? Ya zataji idan taji cewa dan
uwanta shine ubanta, kakarta itace uwarta.?
Ta kalli yaron ta, shi kuma yayan uwarsa shine
mahaifinsa.
Tun da ta dawo bata kara son komawa asibiti
ganin yayan ta mijinta ba.
**** **** **** **** ****
Bayan shekara 6
Jan ne ya warke sumul kamar bashine yayi
hauka ba, sai dai ba gayu ko kalilan tattare
dashi, kana ganin sa kaga ustazu,
Gida ya nufa gun Mamasko ya ci abinci, wani
dan yaro ne da yarinya suka shigo, sun dawo
daga makaranta, suna ta hayaniya,
“Baba kace jainab ta bani book ena”
Janyo hannun su yayi gaba daya ya rungumesu
ya fashe da kuka.
Yau ya zama uban kanwarsa.
Mamasko ce mai bashi hakuri da wa’azi duk
lokacin da abin ya motsa masa, Sabida har yau
idan yace dai tuna abinda ya wuce to Sai yayi
haukar nan tashi, saboda kwakwalwarsa bata
daukar wannan tunanin.
Haka rayuwa ta kasance ma wayannan bayin
Allah, cikin bacin rai da nadama,
Sau dubu Jan ya kalli yaran sai ya tuno abinda
ya faru.
Amma ya rungumi kaddara kada ya aikata
abinda mahaifiyarsa ta aikata Allah ya masa
jarabawar da tafi ta farko.
Hannatu ma ta hakura har ta sake aure chan
kano, sai dai har gobe ta rasa walwarta gabaki
daya.
*ALHAMDULILLAH WANNAN SHINE KARSHAN
WANNAN GAJEREN LITTAFI NA RUGUNTSUMI!!*
A madadin Fiddausi Sodangi dani Hauwa M.
Jabo muke muku fatan alkhairi.
All yasa mu amfana da darussan dake ciki, nasu
hali irin Na Hajiya Kubra Allah yasa su gyara.
Muna godiya da masoyan wannan littafin Allah
ya saka da alkhairi ya bar zumunci sai mun
hadu wani karon.
Gaisuwa ga member NAGARTA WRITER’S
ASSOCIATIONS.
M. Jabo
& Fido sodangi

Comments

Popular Posts