RUGUNTSUMI PART 24..16/2/2017
A firgice Hajiya ta farka a sakamakon
mummunan mafarkin datayi, gaba daya jikinta
ya jike sharkaf da gumi duk kuwa da sanyin AC
daya gauraye d’akin, ido taketa rabawa saikace
an tsare mage a kotu, gaba daya jikinta rawa
yakeyi tamkar mazari
A rikice takai dubanta ga kofa j!in anturo da
karfi, Jan ne yashigo cikin shigar manyan kaya
sai walkiya yakeyi tamkar wani sabon ango, ya
dawo daga turama Hany dinsa kudine ko kallon
ta baiyi ba ya raba gefe ya wuce.
Ita Kam da tunanin ya zatayi da wannan cikin
ta farka bacci, jiki a mace ta tashi ta leka
dakinsa, har ya tube kayan jikinsa, waya yakeyi
Kuma ba alamar damuwa tare dashi, batajin ko
kalma daya da yake fada, ta gaji da tsayuwar ta
ta jiyo jiki a mace ta koma dakinta,
Cikin ta shafa a hankali, tana tunanin ya dace
taje asibiti a duba mata cikin wata nawa ne,
saboda ba wasu alama da takeji na ciki illa
kasala sai tsallaken wata da tayi, shiryawa tayi,
ta fito karo tayi dashi a Palo ya hada tea zai
shiga daki kallon ta kawai yayi ya kauce kansa,
Ya rasa gane mi yasa bai daina son ta duk
abinda ta masa.
Mi yasa yake tsananin tausayin ta.??
Bata damu dashi ba wannan karon saboda tafi
bukatar farin cikin sa akan komai, asibiti ta nufa
ta yiwa Dr. Bayani.
An mata test da duk abinda ya dace, aka
tabbatar mata da cewa ba tada ciki ba alamar
ciki, tayi bakin ciki wani gefe Kuma farin ciki,
Farin cikin ta shine zasuyi aure tunda ba cikin,
bakin cikin ta tana tsananin son cikin.
Ta koma gida ta kai masa result din ta ba yabo
ba fallasa yaji dadi a yanda ya nuna mata.
A daddafe yayi sati daya saboda ya matsu ya
koma gun Hany dinsa,
“Hajiya Ina son naje Nassarawa Na gaida
gida”
Ware ido tayi hadi da kwantowa jikinsa,
“Haba Jalal duk yaushe ka dawo da zaka matsu
ka koma, kodai ka fara gajiya danine”
Ta fada cikin shagwaba,
“No No, Hajiya, Mamasko ce take damuwa akan
nazo kadaici ya mata yawa.”
Haka dai ya cita da dadin baki ya samu ya ya
lallaba ya tafi.
Zaune take saman kujera tana karanta hausa
novel, ta jiyo karar mota amma sanin cewa bai
gaya mata zai zo ba yasa taci gaba da aikin
karatunta, har ya shigo bata ma san ya shigo ba,
tsaye yayi yana kallon ta yana murmushi.
A rayuwarsa ba abinda ke sanya shi farin ciki
duk ya gansa sama da Hajiya Sai Hany dinsa,
Kuma har yau ya kasa tantance son waye yafi
yawa, zai iya cewa Hajiya So ne mai hade da
tsantsar tausayi, ita Kuma Hany So ne da wata
irin shakuwa.
Kamar ance daga kanki kawai taga mutum
tsaye yana kallon ta, wani ihu ta saka tayi tsalle
taje ta rungume sa, cikin shagwaba
“Shine zakazo baka gaya min ba”
Tallabo fuskarta yayi ya tsura mata ido, ya kasa
cewa komai, ya shafa fuskarta ya mata
murmushi,
“I luv u Hany”
Abinda ya iya furtawa kenan, a hankali ta kara
shiga jikinsa
“Luv u too”
Matseta yayi gam jikinsa a hankali yake rada
mata a kunne…
“Ur love is all I crave 4, my heart want more
and more.”
Lumshe ido tayi ta rasa abinda zata fada masa,
bugun zuciyar sa ne ya karu lokacin ta fara
kokarin nuna masa nata salon.
Sun faranta ran juna tsaye a gurin, ya kasa
sakinta Sai kace za’a masa kwacenta, kokarin
kwace kanta tayi, ta nema masa koda ruwan
sanyi ne, kara matseta yayi sosai
“This is ur permanent resident, so stay here till
people take me in their shoulder.”
Toshe bakinsa tayi ta dan daki girjinsa,
“God forbid, kada ka kara fadan haka please.”
Haka dai ya rika sarrafata har Saida ya biya
bukatar sa….
Yana son Hany komai nata burgeshi yakeyi,
Zaune yake ita Kuma ta Dora kanta saman
chinyarsa suna hira, wayarsa ce tayi kara, lokaci
daya suka kalli wayar dake gefe, Hajiya ce ta
Kira, ya kasa dagawa har ta tsinke karo Na biyu
ta sake ringing nan ma bai daga ba,
“Bakaji ana waya bane?”
“Sheeeeeee!!” Ya Dora hannun sa a kan labban
sa, murmushi kawai ta masa taci gaba da abinda
takeyi, karshe silent ya saka wayar.
Saida ya share kwana biyar sannan ya koma
Abuja, ya tafi da shirin neman gidan da zai saka
Hany, saboda ta masa nisa sosai, gashi kullum
yana son ganin ta kusa dashi.
Ya isa gida koda yaje Hajiya tana nan ciki, tun
bakin gate ya fara mamaki ganin bakuwar mota
a gidan abinda bai taba gani ba, ya isa yaji kofa
a kulle gashi baida keys saboda haka sai ya zaga
don yasan ta baya kullum a bude kofar take, ya
shiga ba tare da shayin komai ba, kai tsaye
dakinsa ya nufa ya ijiye kayan sa yayi wanka,
bai tsaya neman taba saboda yasan bata gidan,
fridge ya nufa ya dauko drink mai sanyi ya kora,
dariya ya jiyo tana tashi a dakin Hajiya, Kuma
dariyar mutum biyu ne, mikewa yayi ya leka,
Hajiya ce zaune itada wani Alhaji da gani
dukiya ta zauna masa,
Zuciyar sa ce ta shiga harbawa wani kishi ya
taso masa, wanda yasa ya manta cewa ya taba
shiga farin ciki a rayuwarsa.! Kai tsaye dakin ya
shiga, Hajiya ce ta mike da sauri,
“Jalal! Yaushe kazo?”
Idonsa na kan wanchan dattijon, gadan gadan
yayo kansu,
Kamin ya kara so tayi sauri tace
“Wannan shine Alhaji Bello yayana ne,” burki
yaja jin tace yayanta ne, saidai bai yarda ba,
dago ido yayi ya kalleshi ya dawo da dunan sa
kan Hajiya.
Mutumin hannu ya mikawa Jan, cikin mutuwar
jiki shima ya mika masa hannu, sun gaisa sama
sama ya fice dakin da sauri, a gurguje ta
sallami Alhajin, ta nufi gun Jan.
Tana shiga ya juyo ya kalleta, idonsa sun kada
sunyi jajir.
“Hajiya muje masallaci a daura mana Aure”
Shi kansa baisan lokacin da ya fadi hakan ba.
Dago ido tayi ta kalleshi cike da mamakin abinda
ya fada,
Ta tabbata mayen kishi ne ya dibeshi yake
wannan surutun,
Janyo shi tayi jikinta, nan danan ya sami
natsuwa, baisan mi yakeji akan wannan
tsohuwar ba, wani guntun tsaki yaja.
Bata dai tambayeshi komai ba, haka ta saka
mar ido har ya sauko dan kansa.
** ** ** **

RUGUNTSUMI PART 24..16/2/2017 http://mubarakadamu.blogspot.com/2017/02/ruguntsumi-part-241622017.html
ReplyDelete