RUGUNTSUMI PART 28

“Hajiya mun gano yana zuwa wani gida a
wuse, kullum idan ya fita gidan ki chan yake
wucewa
Yakan dauki awa biyar achan sannan ya wuce
gun aiki, haka kamin yaje gidan ki Sai yaje chan
yayi kamar awa biyu sannan ya fito, assabar da
lahadi ma chan yake tarewa gaba daya, baya
fitowa gida sai Monday da azzahar Sai yazo
gurin ki,
Yana shiga da kayayyaki a gidan dukkan alamu
macece a gidan Amma bamu tabbatar ba, mun
karbo number gidan zan miki SMS dinta, haka
Kuma yana…”
” Enough!!!”
Ta dakatar dashi da karfi, bata tsaya jiran komai
ba ta fito gidan kamar mahaukaciya,saidai bata
san Ina zata nufa ba, wuse ta wuce ta fara raba
ido, Kabeer ta kira saidai wayarsa a kashe take,
zuciyar ta kamar ta fashe saboda tsananin ta
tashin hankali,
“Maman Ummi kece a duniyar nan.”
Idonta ta dago dasu, mutumin da suka rabu ba
girma ba arziki ne gabanta, kamar ta sauke
akansa, saidai Kuma batason ya gane halinda
take ciki, saboda gani take batada makiya a
duniyar nan kamar su.
Murmushi ta kirkiro,
“Haji Sani ya bayan rabo,?”
“Sai khairan Maman Ummi, kin gujemu iya
gaskiyanki, ai Sai ki waiwayomu koda sau daya
ne,”
 A ranta tsaki taja,
“Hmmm abubuwa sun min yawa,”
Ta fada a takaice, idonsa yakai gun tulun cikin
ta, murmushi yayi,
“Gashi Ummi Zata sami kanwa Kema Kuma zaki
sami jika ko.”
Kinsan Ummi tayi Aure tun last year,
“Uhum.”
Bata ce masa komai ba bayan haka,
Zagayowa yayi ya shiga motar,
“nidai sauke ni gidan yata,” bai jira mi zatace
ba, ya zauna ta tada motar saboda ta matsu ta
sallamesa ta tafi aikin gaban ta, ya shiga mata
kwatance har suka isa gidan da zashi,
“Don darajar iyayen ki ki shigo ciki,”
“Malam Sani please bana son shishigi in my
life,
Ka fita Sai an jima.”
Bai koyi motsi ba haka ya shiga rarrashinta har
ta aminta ta shigo ciki. Tana shiga ta daga kai ta
kalli number gidan No 75Q
Suna shiga ta daga kai ta kalleta tsab ta ganeta
yarta ce Ummi.
“Ummi.!”
Wacce aka kira da Ummi ta kalleta ba zata iya
tuna ta ba Amma dai suna tsananin Kama da ita,
duk bacin ran da Hajiya take ciki bai hanata
farin cikin ganin yarta ba, wacce ta yafe shekaru
masu yawa sa suka wuce, saboda son rai irin
nata, nan dai Alhaji Sani ya gaya yarinyar cewa
Maman tace, Hajiya tafi kowa farin ciki da
wannan, taji dadin fitowar ta yau.
Mama bari Na kira muku shi yana ciki kuwa, da
sauri Ummi ta nufi daki don tado da mijin ta,
daidai lokacin sakon Kabeer ya shigo wayar ta,
Kamar ba zata bude ba Sai Kuma ta bude,
*House No 75Q*
Migewa tsaye tayi kamar an mata allurar
mutuwa, yayi daidai da fitowar surukinta,
A hankali ta bude ido ta kallesa,
Suna hada ido ya kasa gane mi yake ciki tsaya
wa yayi komai nashi ya daina motsi.
” *Jalal kaine mijin yata Hannatuannatu* “…..
Ruguntsumi mijinta mijin yarta………

Comments

Popular Posts