RUGUNTSUMI PART18...11/2/2017

Ta nuna masa gaba daya jikinta a mace yake
hatta hannun ta bata iya dagawa wannan dalilin
yasa ya kasa mata komai.
Kuka takeji amma ta kasa yin kukan ji take
kamar ta hadiye zuciya ta mutu, sai ganin
yarinyar takeyi a idonta tana kissing din Mafi
soyuwar halitta a gurin ta.
Wani sanyi ya taso mata, wanda yake hade da
tashin zuciya da sauri ta bude murfin mota
kawai ta fara kwarara amai, kamar hanjin
cikinta zasu fito waje, har saida ta galabaita ya
zama bata iya komai anan gurin, takai minti
goma a gurin dagyar ta samu ta daddafa ta
shiga mota sai dai ta kasa tuka motar, tayi
kokari ta kashe AC ko ta sami sassauci, tayi baya
ta ijiye kanta wani dogon ajiyar zuciya tayi
wanda ke nuna tsananin damuwa da bakin ciki
tattare da it.!
JAN kuwa daga gurin kasa motsi yayi, sai
tunani yakeyi wace kaddara ce ta hadashi da
Hafsa a wannan lokacin?
Yarinyar rabonsa da ita anfi shekara 4 amma
yanzu lokaci daya tazo zata bata masa duk wani
plan nasa,
Har ga Allah baya son bacin ran Hajiya, sannan
bayason abinda zai taba masa ita ko kadan.
Jiki a mace ya sami taxi ta saukeshi gida, abin
mamaki koda yaje bata nan, yayi kusan awa
daya yana leke leke ko zata shigo shiru bata
dawo ba har kusan awa biyu bata ba labarin ta,
Ya gama rudewa, ina ta tafi?
Abinda yake tunani kenan, wayoyinta suna sam
bata dagawa har ya gaji ya daina kira, ya kasa
ci, ya kasa sha, sai safa da marwa yakeyi a
palon, karshe sai yadan kishingida da yake ya
gaji sannan ga damuwa ta mishi yawa, nan
danan bacci yayi awon gaba dashi.
Hajiya ta kare amaye amayen ta, ta sami dan
sassaucin abinda takeji ta tuk’o mota tayo gida,
ganin kofa a bude ta tabbatar da ya dawo gida,
wani kololon bakin ciki ne ya turnuketa da ta
tuna yanda Hafsa ta rika tsutsar bakinsa, rufe
ido tayi amma ina! Saida ta sake wani amai nan
gefen flowers kamin ta shiga palon a daddafe ta
shigo palon, kina ganin ta zaki tabbatar da tasha
wuya sabida gaba daya ta fita hayyacinta, hatta
tsufan da take boyewa da shafe shafe yau ta taji
wuya ya bayyana a fili.
Kwance ta ganshi yana sharar bacci abinsa,
bata iya karanto damuwa a cikin fuskarsa ba ji
tayi kamar ta rufeshi da duka, cikin sassarfa ta
wuceshi dakinta ta nufa, kamar an tsikareshi ya
tashi daga baccin da yakeyi.
“Hajiya kin dawo”
Kamar an mata Allura ta tsaya chak, ta kasa
waiwayowa kuma ta kasa tafiya,
Tafiyanshi taji bayan ta wanda ya tabbatar
mata da cewa yana son karasowa gurin tane,
wani haushinsa taji wanda ya saka mata energy
tuni ta wuce daki cikin kuzari kamar ba itace ta
sharari amai dazuba.
Baiyi kasa a guiwa ba ya biyo bayanta saidai
kamin ya kawo ta datse kofar da key ta shige
dakin.
Samun kanta tayi da rusa wani matsananchin
kuka.
 Ita kuwa ya akayi ta bari son wannan karamin
yaro har ya mata wannan mummunam kamu
haka ?? tabbas idan tayi wasa zai illata
rayuwarta sabida ya riga ya chafko zuciyarta.
Kuka take kamar ranta ya fita.
Yana tsaye bakin kofar yana jiyo sautin kukan ta,
amma kofa a kulle, zagayawa yayi ta dayan
kofar dakinsa wacce take shigowa dakin nasa,
yayi sa’a a bude take tanan ya shigo.
Halin da ya ganta a ciki bama gaskiya bane,
sabida bai taba tunanin haka ta hargitseba.
Yazo kusa da ita zai zauna cikin tsananin kuka
harda majina tace dashi
“Get out JAN! I said get out i dont wana see u
again”
Bai tsaya sauraren ta ba ya nufota ya kamata.

Comments

  1. RUGUNTSUMI PART18...11/2/2017 http://mubarakadamu.blogspot.com/2017/02/ruguntsumi-part181122017.html

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular Posts