RUGUNTSUMI PART 31

Ta mallake mijin da duk wani abu da ya
mallaka, Kuma ita ba boka ba malami da
tsabgegen makirci take tafiyar da komai nata.
haka taci gaba da gudanar da gurbatacciyar
rayuwar ta, tana juya mijin da  danginsa son
santa, gefe guda Kuma tana tare da wasu mazan,
saboda ita bata taba yarda da cewa namiji daya
zai iya biya mata bukatar ta ba.
Duk lokacin da mijin ta yayi tafiya lokacin zata
saka kafa tabar gidan har Sai ana gobe zai dawo
take dawo wa, hakan yasa duk cikin da tayi Sai
ta zubar saboda ita kanta ba zata gane cikin na
waye ba, cikin farko da ta tabbatar cewa Na
mijinta ne bayan Wanda ta zubar shine wata
tafiya da tayi da mijin nata sukayi wata hudu, to
tunda taje bata sami kowa ba da zasuyi lalatar
su, hakan yasa ta bar cikin.
Alhaji shafi’u yaji dadin cikin sosai, hakan yasa
ya dauki son duniya ya daurawa cikin, har Allah
yasa ta haifi cikin, aka saka ma yarinya sunan
maman shi wato Hannatu.
Hannatu ta sami gata a gun mahaifinta fiye da
yanda ake tunani,
Duk da cewa Hajiya Kubra ta haihu bai hanata
bin mazan taba,
Ga igiyar Aure akanta, ga Kuma shegen bin
maza, tun mijin bai sani ba har ya fara zagin ta,
har zargin sa ya tabbata,
Lokacin da ya gane abinda takeyi ba karamin
case sukayi ba saboda yana sonta Kuma yana
kishinta,
Amma ita ko a jikinta,
Kuka ma ta saka masa wai yana tuhumarta da
bin maza, haka dai aka mamushe case din har
Allah ya kara bata wani cikin, shima cikin bata
zubar dashi ba saboda ta san mijinta ne  mai
cikin, saboda a lokacin tadan sassauta bin maza
saboda wannan rigimar da sukayi da mijinta.
ta haifeshi ta sami namiji.
Rayuwar Hajiya Kubra ba abar kirki bace,
saboda tun tana yan mata take bin maza har tayi
Aure bata daina ba,
Taci gaba da tafiyar da rayuwar ta cike da
kazanta ta kwamacala, ana ahaka takuma yin
wani cikin wanda suka sha rigima ita da
maigidan nata akan cewa saita zubda shi, rufe
ido yayi yai mata kaca- kaca amman hakan bai
sa tafasa abinda tayi niyya ba.
Suna acikin wannan hali ne tafiya takama sa
zuwa indiya cike da fargabar tafiyar gudun kada
ya tafi ta zubda mai ciki ya dube ta asafiyar
dazai bar kasar yace “Maman Ummi ina hadaki
da girman Allah kada ki zubda min cikin nan
wallahi Maman Ummi Allah ya aza min kaunar
wannan ciki naki”.
Tun kafin ya kare maganar sa ta katse shi
tahanyar daka mai tsawa
“dallah Mallan rufe min baki! Wallahi
wannan cikin tamkar nacire shi nagama ne!
Angaya maka ni akuya ce ni dazan zauna inta
tara maka y’aya kamar sakara! Salon wahalar
su ya tsofar dani inzama tsohuwar karfi da yaji
ko?” to badani za ai wannan iskancin ba.”
Zaiyi magana takuma daka masa tsawa wanda
yasa shi nufar kofar fita dasauri, har yasaka
kafa awaje yajuyo yace,
“Maman Ummi, idan har kika zubda wannan
cikin Allah ya saka mani duniya da lahira!
ubangiji Allah ya hanaki haihuwa a lokacin da
kike tsananin bukatar shi ko kuma ya baki shi
yakasan ce uban dan ko yar bayada bukatar shi.”
Mikewa tsaye tayi ta nufosa dasauri ya fice ya
bar mata gidan, wannan tafitar dayayi ne
yazamo ajalinsa sunsamu hatsarin jirgi a hanyar
su tazuwa inda babu ko mutum daya daya tsira
acikin su.
Anyi rabon gado kamar yanda addini ya tanada
kubra taci gaba dazama da yaranta acikin gidan
ta, mutuwar mijin ta ya daketa sosai sai dai
bayan wani dan lokaci da tafita takabanta taci
gaba da sharholiyar ta, sam yaran basa samun
kulawa a gun mahaifiyarsu, ana haka yaron
namijin yakamu da ciwo wanda bai kwana ko
daya ba Allah ya amshi kayan sa, sam kubra
bata damuba tacigaba da harkar gaban ta,
arzikinta sai dada karuwa yakeyi domin kuwa
kasuwanci sosai takeyi abinta, ga ta da sa’a duk
wani kasuwanci ta sa saka gaba,
Gefe guda masu kudi suna sonta da aure Amma
sam bata aminta saboda tana kallon Aure a
matsayin abinda yake takura rayuwarta da
kwana da namijin da take bukata, hakan yasa ko
sun nemeta da Aure take mai dashi abin shiririta
da holewa, tayi suna a bariki, dalilin da yasa
dangin mijin sukaga Hannatu bazata samu
tarbiyar kirki ba yasa yan uwan mijin karbar ta,
wanda ba karamin rigima akayi ba, Ganin
batada lokacin tsaya wa rigimar ya yasa ta
sallama musu ita, akan cewa ya murjeshi musu
ita har a bada, ba zata nemeta ba suma kada su
nemeta da yar,
Iyayen ta ma sunyi sunyi Amma Ina ko a jikinta,
mahaifinta da bakin cikin ta ya bar duniya,
mahaifiyarta kuwa tayi-tayi, Amma Ina, addu’a
take Amma ba abinda ke chanzawa, har ta
hakura ta bar ma duniya ita, har Allah ya karbi
ranta.
Bata kula da dangin ta sam, gasu cikin
matsanancin talauci ita kadai ke harkanta.
Hajita Kam Arzikin bana yaci uban nada, saboda
babu kasar da bata zagawa, daga karshe ta
tattara tabar kasar gaba daya, tafi shekara goma
a ingila daga karshe ta tattaro ta dawo Abuja
dazama tacigaba da gudanar da rayuwar ta mai
cike da kazanta wanda ko kare baici, ahaka ne
kuma ta hadu da Jan gundarin rayuwar ta. To
kunji tarihin wannan baiwar Allah.
*** *** *** *** *** ***

Comments

Popular Posts