RUGUNTSUMI PART 25..17/2/2017

Yau lahadi yaune aka daura auren jalal da
Hajiya Kubra akan sadaki dubu hamsin.
An daura auren a masallacin nan unguwar,
Hajiya kam duk ta gaya ma danginta tayi Aure
Amma ba Wanda ta nunawa mijin kawai tace ta
sami wani Alhaji ne zasuyi aure, dama zaman
kanta takeyi.
Batayi wani biki ba illa kara shiri da tayi akan
nada, dama a shirye take to saida ta kara wani,
Sun darji amarci duk da ba sabon Abu bane a
gurin su Amma yanzu sunfi da zakewa.
*****************
Tafiya takai tafiya, yau Auren Hajiya da Jalal
wata goma kenan inda Hany shekara daya,
dukan su ciki suke dashi, Jan ya samu kansa
yana son duka cikkunan kamar ransa Amma
yana tsoron yanda zai fada ma Mamasko yana da
wata mata har da ciki bayan Hany, wannan abin
duk ya tunashi dai yaji bakin ciki, Sai yaji rashin
kyautawarsa ga mahaifiyarsa, ga wani tashin
hankali da yakeji a cikin kansa haka kawai, yafi
kyautata zaton ko asiri aka masa saboda da yawa
suna son Hajiya Amma ta kisu ta Aure shi, Kuma
sun gaya mishi sai sunga bayan sa.
Uwa uba gashi yanason ya dawo da Hany Abuja
saboda ta masa Nisa sosai, Hajiya tun tana
complain akan yawan zuwansa gida har ta daina
yanzu ta saba, duk weekend yana hanyar garin
su.
Ya dukufa neman gida har Allah yasa ya samu,
Yanzu ya Sami gida madaidaici a zone 4, anan
zai tare shida madam dinsa Hany. Tunda ya
gayama Hany zasu koma Abuja murna kamar ta
kasheta, saboda dama ta tsani yawon hanyar da
yakeyi duk sati, nan ta fara shirye shiryen
komawa Abuja, ga cikin ta da ya dan turo zai Kai
wata shida zuwa bakwai, baisan ita da Hajiya wa
zai fara haihuwaba.
sun dawo Abuja cikin nasara, saboda duk abinda
yake tsoro ko daya bai faruba, Hajiya bata gane
komai ba, dan yanzu gaba daya dukiyarta tana
hannun sa, shi yake tafiyar da komai. Sai dai
matsala daya ya zai raba musu kwana ba tare da
wanin su yayi zargin wani Abu ba,
Hany bata ganin sa da dare Sam, saidai da rana
yazo yayi abinda zaiyi ya koma gun Hajiya, Sai
assabar da lahadi yake kwana gida, shi Kuma Sai
yace ma Hajiya ai yana tafiya gun Mamasko ne.
Jan kenan mai Hajiya da Hany.

Comments

Popular Posts