RUGUNTSUMI PART 14..7/2/2017...10:00 PM

Cikin daure fuska yace
“Muje idan ka kare dariyar ko,”
Ahmad bai daina dariya ba yace
“Hope ka karbo numbar ta, sabida nasanka
akwai nasarar samun number mnyan kaya,”
Ya fada yana kokarin bude motar ya shiga,
banza JAN ya mishi,
Jabir ya kalleshi
“Ya kukayi da ita my Man?” ya tambaya cikin
nuna kulawa, key ya yiwa motar sannan yace,
“Wallahi bata kulani ba amma dai nan ne gidan
su gobe zamu dawo ko?”
Ya fada yana kallonsa,
Murmushi Jabir yayi
“sosai zan rakoka ko banza zansha AC ”
dariya sukayi gaba dayan su, har suka isa ban
tanka Ahmad ba, shi dole fushi yakeyi dashi.
Washe gari JAN bai ma nemi Ahmad ba Jabir
kawai yama waya suka dau wanka basu tsaya ko
inaba sai gidan da ya ga Hany dinsa ta shiga.
Da motarsa ya tafi dan kada a raina masa
wayo.
Baba maigadi yama magana ganin sa da mota
ya fara washe baki yana masa kirari, bai bata
lokaci ba ya sallamesa ya kuma gaya masa
bukatarsa,
“Ai dan saurayi ita hannatu ba yar nan bace,
yar kano ce da sunyi hutu take zuwa nan, da
yake akwai yan mata a nan gidan sai suyita
yawo a gari”
Ya karasa yana washe baki,
“To baba yanzu ya zan sameta kenan?”
“Eeh to! Kasan yaran zamani amma bari na
shiga ciki na gani”
A dudduke mai gadi ya shiga gida yana sake
saken yanda zai fuskanci lamarin, dama ya saba.
“Hannene Hanenne”
Hannatu yake kira yana washe baki,
Tana ganinsa tasan anzo wurin tane,
“Yadai baba mai gadi? Da wace kala yazo yau?”
Yayi dariya sabida ya gane mi take nufi.
“Ai ina gaya miki irin wannan ce kunburarra,
mai kan jirgi, gaban ta da bayan sun tafi sitiree”
Ya fada yana mike hannu alamar stret.
Kwashewa sukayi da dariya gaba dayansu,
“To baba zan iya fita masa haka ko sai na
chanza kala?”
“Ai kawai ki shiga ciki ki saka yan kayan nan
masu mai dake yar charas chas.”
“Heheee baba kace babban kamu zanyi” ta fada
tana wucewa daki da gudunta.
” yauwa ki shafa wannan abin na saman ido ki
labta jan baki Hannenena”
Hajiyar gidan ce ta fito sauri yayi ya kame dan
yasan fada zata masa, sum sum ya fice.
Da yake yasan halin Hannatu yana fitowa yace
ma JAN.
” Ai yallabai ka taki sa’a yanzu koda na shiga
tana shiryawa zata unguwa kaga sai ka gyara da
ta fito sai ka tareta ku sossoye”
Dadi JAN yaji ya kara sallamar baba mai gadi,
baba ya wuce yana ta murmushi.
Ba’a kai minti hudu ba sai gata ta fito tana ta
fadace fadace ita ala dole wani take jira baizo ba
har yanzu.
JAN ne ya fito daga cikin mota yana taku irin na
mazan da suka san kan duniya.
Da murmushi ya karaso gunta, ita kuwa kamar
batasan ma da zuwan sa ba, ta ganeshi sarai
kawai basarwa tayi, kirjinta ne yake dukan uku
uku lokacin da yake kokarin karasowa gunta.
Yanda take jinsa bata taba jin wani saurayi
hakan ba, ji take kamar ta ruga sabida abinda
takeji aranta tace wannan wane irin abune farat
daya ko jiya fa haka ta rikaji, shima a nashi
bangaren abinda yakeji game da ita kenan
kamar dai yanda yake jin na Hajiyarsa.
Sallama ya mata, cikin natsuwa ta amsa dan
kada ya gane yanayin da ta shiga,
Wayarta ta dauka ta fara fake call.
“Haba Yaya tun dazu fa kai nake jira muje
Jabonation Mall, amma har yanzu baka zoba
Allah wucewa ta zanyi na gaji da jira.”
Bata jira komaiba tayi kamar ta kare waya ta
saka wayar cikin jaka.
“Kinga kuwa nima Jabonation Mall din zani, sai
muje na karasa dake ko?,”
Cikin yanga ta amsa da
“No nagode yaya zaizo ya kaini”
Haka dai JAN yayi amfani da duk wasu makamai
nashi har saida yayi nasarar daukarta zuwa
Jabonation Mall din, a hanya ne suke dan taba
hira har suka karbi number junansu.

Comments

Popular Posts