RUGUNTSUMI PART 9..02/02/2017
Tun da yaji maganar hajiya akan wata mace
yasan cewa tana da kishi, haka komai ma
zata’iya aikatawa akanshi, ganin haka yasa yayi
Alwashin bazai kara zancen wata gaban ta ba,
koda kuwa Mamasco ce.
JAN da Hajiya sun d’and’ani zumar junan su, ta
yanda ba abinda zai iya rabasu da juna sai dai
mutuwa, saboda suna baiwa junan su kuluwa ta
musamman.
Da kyar ta barshi ya dawo gida.
Bayan ya baro Abuja da sati daya.
Hajiya ta kasa hakuri da rashin sa kusa da ita,
haka tayo balaguro har Nassarawa ta biyoshi ta
kama Hotel, anan suke holewarsu son ransu.
*** *** ***
JAN shida Mamasco suna hira kamar yanda
suka saba duk daren Allah, saboda duk dare sai
sunyi hira shi da tsohuwarsa, duk son da yake
yiwa Hajiya Kubra baya iya barin Mamasco yaje
gunta ya kwana, sai dai su yini tare, tun safee
idan yasa kafa ya fita baya dawowa sai dare,
hakan yasa Mamasco bata gane komai ba,
saboda baya kwana chan, ranar ma da taga
sammakon nashi yayi yawa take tambayarsa mi
yake fita yayi a waje tun safe har yau assabar da
ba karatu. sai yace mata kawai duk yana
k’ok’arin cika takardun komawa Abuja ne, ita
kuwa sai tayi ta zuba masa addu’a da fatan
Alkhairi.
Kamar kullum yau da dare ya dawo a gajiye,
saboda hajiya bata bari ya huta ba, saboda
tsabar jaraba irin ta
Hajiyarsa.
“Mamasco komai fa ya kankama, jibi ne zan
wuce Abuja karatu na.”
Ya fada yana kallon fuskarta.
Mamasco cikin jin dadi tace
“To Jalaluddinina, Allah ya taimakeka ya baka
sa’a a dukkan lamuran ka,”
Cikin farin ciki da murnar addu’arta ya amsa da
Amin.
Ta mishi nasihohi akan ya kula da kansa da
karatunsa kada ya biyewa mutanen Abuja
karatunsa ya lalace, batason tarbiyar da ta masa
ta gurbace.
Ranar da yamma ya fara har hada kayan sa
domin tarewa gurin muradin rayuwarsa.
Tunanin Mamasco daya ina zai rika samun kudi,
musamman rayuwa irin ta Abuja mai tsada. Data
masa maganar, cikin kulawa yace,
“Kada ki damu Mamasco, makarantar tamu, su
zasu dauki nauyin komai nawa, zasu bani duk
abinda nake bukata, sannan kinga inada
diploma, da ita zan nemi aiki, kinga ko anan zan
iya samun kudin da zan rika wasu lalurorina
dasu”
Baki washe tace
“To Allah ya shige maka gaba ya baka sa’a a
rayuwarka.”
Ya amsa da amin.
Ta tayashi sun hada kayan sa gaba daya, bayan
ya kare yaje gidan yayarsa ya mata ban kwana
kuma ya roki yayar tashi akan ta baiwa
Mamasco Zainab ta rik’a tayata zama da taimaka
mata da yan guntayen ayyuka, kada ta zauna ita
kadai kadaicin zai mata yawa.
yayar ta aminta da hakan, tace masa da mijinta
ya dawo zata gaya masa, duk da cewa tasan zai
aminta amma sai ta gaya masa sai a kawota.
Hakan yafi dacewa mata sunayi bawai dan
kinsan mijinki yana aminta da abu ba, sai kawai
ki aikata, No idan dai yana da hakki to dole ne ki
sauke hakkin nasa kamin ki zartar da hukunci,
saboda zaki iya aikata abinda bai kai ya kawo ba
amma shi kuma ganin yanada hakki ba’a gaya
masa ba sai yaji haushi har ku sami sabani.
Mamasco ta bashi kudi masu yawa amma sam
yaki karba, har saida yaga tayi fushi sosai
sannan ya karba, a ransa ya raya cewa da yaje
bada dadewa ba zai dawo mata da kudinta akan
ya sami aiki ne.

RUGUNTSUMI PART 9..02/02/2017 http://mubarakadamu.blogspot.com/2017/02/ruguntsumi-part-902022017.html
ReplyDelete