RUGUNTSUMI PART 26.

Hajiya ce kwance saman sofa tana lallatsa
wayarta mantuwa tayi da wasu kayan ta da tayi
order kusan shekara daya aka tsaresu a border
dazu an gaya mata an sakesu, jiki na rawa ta
tashi ta tura cikin ta tayo cikin dakin sa, abinda
ya fado kunnen tane yasa ta manta mi tazoyi
dakinsa.
“Ooh my Hany I will send U”
“My Hany”
Maimaitawa tayi cikin hade girar sama data
kasa,
 Murmushi ya sake mata, ya ware hannuwansa,
ta kasa masa musu ta fada jikinsa ya
rungumeta, ya shafa cikin nata yayi kasa da
kansa ya dora a cikin,
“Yaron Dady yaushe zakazo? Kaga Dady?”
Cikin sa’a kuwa cikin ya motsa,
“Laaaa kaga yana motsi, yaji abinda kake
fada”
Dariya ya Sako, Wanda ya kara fitar da kyansa,
“Yaron Dady yasan Dady nasa, kayi sauri ka fito
inason ganinka,”
Cikin motsi ya karayi, batasan lokacin da ta
wangale da dariya ba, gaba daya ta manta da
zancen wata Hany da taji ya fada.
Haka ya mantar da ita zancen Hany gaba daya,
har ta gaya masa abinda tazo fada masa, sunyi
akan zai tura yaransu suje su dauko kayan.
Bayan sati uku.
Shigowar Jan kenan daga gidan Hany wacce ciki
ke bata wuya yanzu, sam batayi laulayiba sai
yanzu take yinsa, tare yake shida abokinsa
Ahmad wanda yakawo masa ziyara daga
Nassarawa, da yake Ahmad yasan komai shi
kadai yasan Jan ya Auri Hajiya,
sauri yakeyi yashige dakinsa tunkafin Hajiya ta
fito ta iskoshi, dan kuwa jikinsa inbanda kamshin
turaran Hany babu abinda yakeyi, zaune yabar
Ahmad a falo yana duban TV. Tun kafin
yakarasa dakin yaji muryar Hajiya na fadin
“oyoyo sweet Jan sai yanzu kashigo nagaya maka
bana son wannan sabon halin daka dauko nayin
dare awaje!”
Rungumosa tayi ta baya tana shakar kamshinsa,
Dasauri tasake shi tare dayin baya tana zazzare
ido, gaban sane yayi mummunar faduwa, cikin
garaje take magana
“Jalal daga ina kake? daga ina kake nace ka
gaya min daga wajan wata yar iskar kake?”
magana take tana haki tamkar wacce taci uban
gudu,
Na dade Ina Kula da chanjinka idan nazo
tambaya Sai ka dauko min wani zance daban.
Duk kwana kinnan haka take tirtse shi da
tambaya wata ran idan tasoma fada zaku zaci
hauka tasoma yi,
Yau Kam ba sauki saboda ta hau sosai, kwalar sa
taci hade da makure sa cikin hargagi take fadin
“Jalal baza ka gaya min ina kake zuwa ba
kowani dare?”
wannan shine karo na farko dayaji tsanar ta ta
darsu a zuciyar sa, amma Kuma still akwai
tausayin ta kwance a cikin zuciyarsa, da idan
tanayi yana zaton tsabagen son datake masa ne,
ayanzu kuwa dauka yake tsabagen hauka ne
dason zuciya irin nata, wani munafukin
murmushi yasaki irin na mayaudaran maza,
cikin murya kasa kasa nawanda yasha shaka
yashiga fadin
“haba Hajiyata tayaya ki ke tunanin zan iya
kula wata mace aduniya bayan ke? Mai kamar
ki mezaiyi dawata Mace aduniya? Aini wallahi
kin isheni rayuwar duniya, banga macan dazan
duba inmata duban mace ba! Inaso ki kwantar
da hankalin ki kidaina damun kanki dani danni
banida matsala kodaya!”
Harara ta sake masa
“Jalal a haife Na haifeka wallahi, saboda haka
kada ka nemi ka raina min wayo”
Kashe mata ido daya yayi ya daga gira,
“But yanzu dai ni Mijin kine uban yayan ki,”
Sasautowa yayi kasa ya shafi cikin
“Yaron Dady kaga Mum dinka tana nema ta
kashe maka Dady ko,”
A hankali cikin nata ya shiga motsawa, Baki
Hajiya ta washe tareda sakinsa tana fadin
“Wannan yaron da kishin Dadyn sa yake, da ka
kawo karata Sai ya shiga nusata,”
“yauwa dan halas, shiyasa kake burgeni nake
alfahari dasamun ka a matsayin abokina Kuma
dana, Kaci gaba da mata wrestling a ciki” dariya
suka saka gaba daya,
Juyowa tayi ta fuskanceshi,
“,My Jan! Ni macece mai tsananin kishi
yakamata kadinga kiyayewa dan Allah,”
rungumota yayi a jikinsa yana fadin,
” bakida matsala dani Hajiyata ki kwantar da
hankalin ki wani sabon shop muka shiga nida
Ahmad shine na dau turaran nadan fesa inji
inyanada dadin kamshi sau daya ma na fesa
Ahmad yace min ai wannan turaran na mata ne
shine namaida na ajiye bama musaya ba muka
fito,”
nan danan Hajiya tasamu natsuwa a zuciyar ta
tayarda da abinda Jan yagaya mata, zuciyar ta
fes! Duk da cewa ta dade tanajin yana wannan
kamshin, Murmushi Jan yayi Yana mata wani
irin duba mai wuyar fassarawa!
Ahmad dake zauna yana duban su yana Kuma
sauraran abinda ke faruwa yayi gyaran murya
wanda yasa Hajiya saurin juyowa dan sam ta
manta da wani a palon, gaban Jan yai mugun
faduwa dan yafi kowa sanin halin Ahmad da iya
gulma tamkar mace, dan haka yayi saurin tsare
shi da shanyanyun idanuwansa masu kama da
kalar bacci, dole Ahmad ya hadiye abinda keson
fitowa daga bakinsa badan yasoba, yashiga gaida
hajiya cikin fara ‘a ta amsa tana wage baki……….

Comments

Popular Posts