RUGUNTSUMI PART 30

Kuka mai sauti,Shin da wanne zaiji, da
surukarsa matarsa ko kuma Yar matarsa Kuma
matarsa.
Karo Na farko da ya fara dana sanin abinda ya
aikata,
 Haka suka kasance a gurin, Hany ta dawo abin
tausayi lokaci daya har ta chanza kamanni, Jan
da baya ma son ya dago kai ya kalli Hany, ya
kwana da uwarta ya kwana da ita, sannan duk
suna dauke da cikin sa, dafe kai yayi iya karfinsa
ya cije lebensa, wasu konannun hawaye ne suka
fito masa, hadi da wata kara kamar mahaukaci
sabon kamu……
TUNA BAYA….
 “Baffa ni Kurba zan Aura”
Alhaji shafi’u ne yake fada ma mahaifinsa cewa
Kubra yakeson ya aura, Amma mahaifinsa yaki
aminta da hakan sabod rashin kamun kan
Kubra,
“Shafi’u bawai bana son farin cikinka bane,
nima zan so ka auri duk wacce kake so,Amma
yana da kyau ka gane mace ta gari tafi komai
dadi a duniyar nan, sannan zaka sami yaya Na
gari ta hanyar ta, yarinyar nan kowa yasan
gantalalliya ce ga uban kwadayi da yake
damunta haka zaka….”
Katse mahaifinsa yayi ta hanyar dakatar dashi da
hannu.
“Baffa ko wace iri ce ni Ina sonta Kuma zan
Aure ta.”
Yana fadar haka ya mike ya wuce yabar iyayen
sa zaune,
“Kin dai ji yanda mukayi dasu”
“To kenan ba zaka Aure ni ba?”
Ta fada cikin muryar yaudara,
“Zan aureki mana, ai tunda iyayen ki sun
amince shikenan banida burin da ta wuce Kasan
cewa tare dake”
Haka sai Kubra da shafi’u suka nace akan Sai
sun auri juna iyayen shafi’u basason auren sam
haka dai aka lallaba aka kai amarya dakinta,
Zaman su suke cikin kaunar juna da baiwa juna
kulawa har Na tsawon wata daya,
Mafarin rigimarsu shine cikinta Na farko, ita
batason ciki shi Kuma yana son ciki haka ta
sakashi gaba da cin mutunci, karshe tayi yan jike
jikenta na gargajiya ta zubar da cikin ta na
farko.
Sunyi rigima sosai daga baya ya hakura,
Ya maidata gun su baffa lokacin da tafiya ta
Kama shi kasar tura domin gudanar da ayyukan
sa Na yau da kullum.
Kubra ba tada jinkirin rashin namiji kusa da
ita, hakan yasa ta fara tunanin yanda zata rika
fita waje dan kawar da sha’awarta, ta kuwa
samu, dan tana zillewa taje waje tayo yawon ta
zubar dinta ta dawo, har takai tana lalatarta da
kanin mahaifin mijin ta, har takai ta samu ciki
dashi kamin mijinta ya dawo, nan dai tayi yanda
tayi ta zubar da cikin nan.
Kubra bata zamo suruka ta gari gun surukanta
ba, kullum cikin ci musu mutum ci take, masifar
safe daban ta yamma daban.
Haka har mijinta ya dawo daga tafiyar da yayi,
cikin nasara saboda ya samo alkhairi mai tarin
yawa, haka ta shiga ta fita ta hana iyayen
mijinta komai.

Comments

Popular Posts