RUGUNTSUMI PART 16...9/2/2017

Tafiya tayi tafiya JAN da Hajiya an zama daya,
duk tafiye tafiyen da takeyi dashi take tafiya, shi
kuwa yana biye da ita kamar jela, gata kam yana
samunsa bako kadan ba, motsi idan yayi a
idanun hajiya yake yinsa, tabi ta kasa ta tsare
kuma har rakawa takeyi, tana biye da duk wani
moving nasa tana bincike, a skull a kwai masu
saka masa ido haka idan ya fita motsa jiki tana
sawa ana bibiyarsa, kusan wata bakwai bata
taba kamashi da wani abu da ya sabawa tsarinta
ba, wannan dalilin yasa ta daina bibiyarsa tasa
aka daina kula dashi ta aminta dashi 100%.
uwa uba da so da kauna da yake nuna mata hadi
da kulawa, wanda yafi komai mata dadi a
rayuwarta.
Ta fara tunanin mika masa ragamar
dukiyarta, amma idan ta tuna wasu abubuwa sai
ta fasa.
JAN ne kamar yanda ya saba fita ya dau wanka
kamar yanda Hajiyarsa ke bukata, ya fito suna
tafiya tare da Hajiya suka shiga wani Mall kowa
yana gefen yana zabar abinda yakeso. Charaf
idonsa suka fada akan Hafsa, sanin halinta yasa
yayi kokarin boyewa, amma ina, kamin ya kauce
tuni ta hangoshi, iya karfinta ta kwala masa kira
“JAN.!!!” Da gudunta taje ta rungumeshi, tsoro
hadi da razani ya kamashi, Hafsa dai tsohuwar
budurwar sa ce da sukayi Diploma tare, daga
nan ta wuce Cyprus karatu, tun daga lokacin
basu kara haduwa ba sai yau, sun gurji duniya
ita dashi, Hafsa irin yan matan nan ne da basuda
kunya bare tsoron Allah, ko gaban mahaifinta
zata iya rungumar namiji, saboda bata dauki
haka a bakin komai ba illa wayewa,
Da sauri yayi kokarin banbareta jikinsa kada
hajiya ta gani, amma ina har Hajiya ta hangosu,
bata sakeshi ba saida ta sunbaci kumatunsa, duk
a idon Hajiya,
ta sakesa ta dafa kafadarsa tana dariya,
“JAN kalli yanda ka zama babban yaro,” ta
kallesa daga sama har kasa tana murmushi,
“Hmmm naga bakayi murna da ganana ba at
all.”
Ta fada tana lumshe idonta, Hajiya ce tayo
kansu gadan gadan, da yake ya bata baya so
bazai iya hango Hajiya tana tahowa ba, Hafsa ce
kawai ta ganta, Hannun sa ta janyo
“Dallah muje waje Alkah JAN m miss u much,
what of u?”
Ta fada tana janyo hannunsa suka bar layin
kamin Hajiya ta kawo har sun bar gun, haukace
kawai hajiya batayi ba, kamar zararra haka ta
biyosu tana wani wawan sauri.
Hafsa kuwa har tana kokarin jantoshi su fita ta
sami gu suka zauna cikin fari da ido tace
“Oya kana mamakin ganina ko shiyasa ko
magana ka kasayi tin dazu”
A hankali ta tashi tsaye ta janyo kumatunsa da
hannuwanta ta turo baki alamar tana masa kiss.
Daidai lokacin Hajiya ta kawo zuciyarta tana
tafarfasa, bata tsaya bata lokaci ba
Ta wanke Hafsa da wani bahagon mari.
Hafsa dagyar ta iya bude idonta sabida saida
taga taurari da aka mareta din nan.

Comments

  1. RUGUNTSUMI PART 16...9/2/2017 http://mubarakadamu.blogspot.com/2017/02/ruguntsumi-part-16922017.html

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular Posts