RUGUNTSUMI PART 12.. 4/2/17

Watansa uku kenan gun hajiya, ta mayar dashi
kamar mijinta duk lokacinda take bukatarsa zata
nemeshi shima hakan, wani abu da suke
fuskanta kuwa shine duk lokacin da suka kare
lalatarsu sai su rik’ajin sunyi ba daidai ba,
wannan dama duk mai aikata aiki mara kyau
yanajin hakan sai dai kawai yaci gaba da
aikinsa.
Karshen wannan watan ya shirya tafiya gida,
saboda Ahmad yana matsa masa sosai, idan yana
tare da Hajiya har Mamasco mantawa yakeyi da
ita.
ta hanashi tafiya saida ta fara period da tasan
cewa ko yana nan ba abinda zai iya mata sannan
ta barshi ya tafi, akan sati daya zaiyi ya dawo.
Ya shirya ya hada tsofaffin kayan sa akan zai
kaiwa abokansa da suke zama tare a dabar su,
da duk wani tarkace nashi ya wuce sai gida.
Da motar sa yaje saboda su sami ta fasawa, sai
dai baiyi gigin karasawa da ita gun Mamasco ba
saboda zata titsiyeshi akan ina ya sameta, hakka
kaya masu tsada bazai bari ta gansuba kada tayi
zargin wani abu. duk wajen su Ahmad ya barsu
ya isa ma Mamasco da kaya niki niki.
Murna a gurin ta ba’a ko magana.
Sunyi hira sosai na yaushe rabo, dama d’a da
mahaifi sai Allah.
Yawo sukeyi shida Ahmad da jabir a motar sa,
yanzu kam basa fita da motar Ahmad, da motar
JAN ake yawo, sun zaga gari sun ci kudi anje gun
tsofaffin yan matan sa da kawayensa.
Yau Kwanan sa uku a Nassarawa, ranar sun fita
zaga gari a hanyar sa ta zuwa gidan mai saboda
man motar tasu ya kusa karewa, Jabir ne da
karfi yace,
“Kuut yaseen itace!”
Gaba dayan su suka waigo suka kalleshi, suka kai
duba gunda suke ga yana kallo,
Gaban sane yayi mummunan faduwa lokacin da
ya hangota. Da karfi sa yace,
“Yes itace. Yeah! Yeah!! Yeah itace!!! ” abinda
ya rika fada kenan yana jinjina kai, har yasa
suka juyo suna kallonsa.
“Kai JAN kada ka kashemu mana”
A hankali ya dawo daga kallon ta, yama manta
da cewa tukin mota yakeyi, ya kalli Jabir yace
“Jabir itace fa!”
Jabir yace
“Eh ina ganin ta na tunata.”
A hankali ya fito motar suma suka fito suka
tunkareta basa shayin komai.
Tsaye take tana waya tana ta murmushi.
Da ganinta kasan tana cikin hutu, shigar jikinta
ta bayyana tarbiyanta.
Bugun zuciyar JAN take tsanan ta lokacinda
suke dada matsawa kusa da ita.
Tsayawa chak yayi lokacin da ta dago idonta ta
kalleshi hadi da wani lalataccen murmushi, mai
nuna natsuwa, wanda shi kansa yasan wannan
murmushin ba nasa bane saura kiris ya kife a
gurin lokacinda yaji tace
“Luv U 2 ma bobo”

Comments

  1. RUGUNTSUMI PART 12.. 4/2/17 http://mubarakadamu.blogspot.com/2017/02/ruguntsumi-part-12-4217.html

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular Posts