RUGUNTSUMI PART 27

Hany zaune tana hada wasu kaya da suka siyowa
baby jiya, wayar Jan ce tayi kara, bata kulaba
dan ya mata kashedi akan kada ta kuskura ta
taba masa waya, mamaki ma take ya akayi Jan
ya bar wayarsa ya shiga wanka,
Bata kula ba haka har akayi Kira Na biyar, ta
tashi ta dauki wayar ta nufi hanyar bayi ganin
an sake Kira Kuma an rubuta *Hajiyata* yasa ta
daga wayar, saboda tayi tunanin Mamasko ce,
“Hello Hajiya Ina wuni”
Gaban Hajiya ne ya fadi jin mace ta daga saidai
jin tace Hajiya yasa bata kawo wani dogon Abu a
ranta ba,
“Lafiya yau, Ina Jalal yake ne”
“Eh yadan fita ne yanzu zai dawo Amma”
“Ok” sai ta kashe wayar.
Bata natsu ba sam ta kara Kira,
Hany cikin ladabi ta kara daga wayar,
“Yarinya wacece ke?”
Hany Murmushi tayi wato dai Mamasko naji da
Jan, Sai taji ko wacece,
“Hajiya nice fa.”
“Nice Hannah,”
“Ke wace hannatu Kuma, ”
” Hajiya nice fa Matarsa”
Gaban Hajiya ne ya fadi tuni idonta suka chanza,
Jan ne ya fito ya kalleta mika masa wayar tayi
tana kokarin goge masa ruwan jikinsa da towel.
Dakatar da ita yayi hadi da daka mata wata irin
tsawa,
“Uban wa ya Baki damar daukar min waya
harda fadin ke mata tace?”
Wannan tsawar tayi sanadiyar murdewar cikin
ta,
Bai kashe wayar ba Kuma Hajiya ta jiyo abinda
yafada.
 Wurgi yayi da wayar ya fara safa da marwa a
dakin, idonsa sun kankance lokaci daya, hannu
yasa ya dafe kansa, bai tsaya kula Hany ba data
durkushe a gurin, da sauri ya saka kayan sa Sai
gida.
 Hajiya ya gani tsaye kamar an mata mutuwa,
jikinsa ne yayi sanyi, dafe kansa yayi ya juya zai
fita saboda yasan mai faru wa ta Riga ta faru,
Daga baya Hajiya ta riko rigarsa,
“Wacece Hannatu Jalal”
Dago Kai yayi Yana kallon ta, idonsa sun chanza
gaba daya, baice da ita komai ba, gurgiza kai
yayi,
Ya bukaci ta sakesa, Amma ya kasa, janyota yayi
jikinsa,
 Nan ta shiga rera masa kuka mai tsuma zuciya,
yayi rarrashi har ya gaji, batayi shiru ba,
Daga karshe kwantar da ita yayi ya zauna bakin
gado, ya dade dafe da kansa, daga karshe ya
bar gidan gaba daya, yana fita ta janyo wayarta.
“Hello kabeer, don Allah jalal nake son ka kula
mun da shige da ficen sa duk inda zashi a rika
binsa har a tabbatar min da abinda yakeyi Ina
yake zuwa.”
“An gama ranki ya dade”
Bata jira komai ba ta kashe, Saboda tsab zai cika
ta da surutai.
Ya koma gida Hany ya gani takure gurin da ya
barta, bata dago kai ta kallesa ba, tausayin ta ya
Kama shi, yazo ya fara rarrashinta itama,
“Miyasa zakaji haushi dan Na daga wayar
Mahaifiyarka”
Taci gaba.
“Da ace banga an rubuta Hajiyata ba wallahi
bazan taba daga wayar kaba, but kayi hakuri
kaji”
 “Ya wuce ki daina damuwa”
“Amma naji muryan Mamasko ta chanza, bata
ma fa ganeniba Saida nace nice matarka.”
Numfashin sane ya tsaya Chak.
A hankali ya runtse idon sa, baice mata komai
ba, baya yayi da kansa ya kwanta ya fada tekun
tunani.

Comments

Popular Posts