RUGUNTSUMI PART 32
Anyiwa Hajiya aiki cikin nasara an fiddo mata
kyakkyawar diyar ta Mace mai cike da koshin
lafiya, ankai ta wani daki inda aka sanar dasu
Jan cewa zasu iya shiga suga Yar da aka haifa,
sai dai abin mamaki babu wanda yayi yinkurin
zuwa ganinta daga mijin har y’ar,
Hany jikinta ke rawa tana wani numfashi sama-
sama kai da gani Kasan bata cikin hayyacinta, ko
motsi batayi ba illa wata ziza da take mai Kama
da kukan yara.
kawun ne yayi karfin halin shiga dakin dan yaga
halin da take ciki, yasame ta tanata sharar
baccin ta fuskar nan tata tayi fayau, jikinsa a
sanyaye ya dauki diyar ya tsura mata ido,
tsawon lokaci yana rike da y’ar yana sake sake
a zuciyar sa jiki ba laka ya ajeta tare da zaro
wayar sa ya kira can garin dumin yasanar dasu
halin da ake ciki, waje yakoma yasami su Jan
har yanzu acikin hali na kidima, nasiha yashiga
yimasu mai ratsa jiki, daga karshe yasanar dasu
gobe insha Allahu sau ran dangi zasu iso dan
asan yaza ayi a warware wannan babban
matsala, cikin kuka Jan yace dan Allah kawu a
biya a dauko min mahaifiyata domin in roketa
gafara nasani hakkin ta bazai barni inzauna
lafiya ba yakare maganar cikin matsanancin
kuka abin gwanin ban tausayi.
Haka wayan nan bayin Allah sukai kwanan bakin
ciki babu wanda ya runtsa acikin su, musamman
Hany da tafi Kama da zararriya, da ka ganta
zaka fahimci hakan.
Washe gari misalin karfe hudu na maraice
dangin hannatu suka iso tare da mamasco wacce
duk ta rikice dajin wannan mummunar labarin,
Tundaga harabar asibitin gaban Mamasko ke
faduwa tamkar zai fado kasa Jan na ganinsu
hankalin sa yakara tashi bama kamar daya hada
ido da Mamasko ba, tuni yanemi natsuwarsa ya
rasa ji yake tamkar ya sheka da gudun tsiya,
Hany ta mike a guje ta fada kan kakarta tana
kuka mai tsuma zuciyar mai saurare,
A haka suka dunguma zuwa cikin daki inda uwar
gaiyyar ke a ciki a kwance tuni ta dade da
farkawa sai kuka takeyi tamkar ranta zai bar
jikinta.
Ahaka suka shigo dakin gaba dayan su bakin
su dauke da sallama, Mamasko itace tazama kar
shan shigowa, ido hudu Mamasko tayi da Hajiya
Kubra, wani irin salati Mamasko tasaki ta nuna
ta da yatsa hade da yanke jiki tafadi Hajiya
Kubra wacce tayi mutuwar zaune tuni ta rikice
jikinta yahau kyarma bakinta na rawa tashiga
fadin wacece wannan!?” babu wanda yabi ta
kanta tuni Sun rufa akan Mamasko wacce tayi
dugowar suma, Hany ce tabawa uwar ta amsa
jin bakinta yakasa daina furta wacece wannan
datake ta fadi, kuma da alamun ta kagu taji
amsar tambayar tata, “Mahaifiyar JALAL ce” ihu
Hajiya Kubra tasaki tana fadin “Kada dai kuce
min JALAL DAN WANNAN MATAR NE……..”

Comments
Post a Comment