RUGUNTSUMI PART 29

A rikice Hajiya Kubra ke nuna sa da yatsa
tana fadin,
” Jalal kaine mijin yata Hannatu?
Innalillahi………”
bata karasa ba tayi k’asa rike da kugunta tana
fadin ”
“Washh! Wash!!” Da gudu Jan yayo kanta yana
fadin “subuhanalillahi Hajiya! Hajiya!!” Tuni
tafita haiyacinta sai wani irin nishi takeyi tana
cije baki, gaba daya Jan ya rude ya rikice sai
faman tambayar ta yakeyi “Hajiya Meye ke
miki ciwo,baya ne?” Saboda lokacin da Hany ta
kirasa bata gaya masa cewa mahaifiyarta bace,
shi ya dauka tsabar kishinta ne yasa ta wannan
binciken.
“Ko cikin ne?”
duk a gigice yake jero mata wayan nan
tambayoyin,
“Hany wacce tayi mutuwar tsaye saboda
tsabagen Al’ajabi da mamakin ganin halin da
wacce aka kira da mahaifiyar ta tayi a
sakamakon ganin mijin ta da tayi, sai a wannan
lokacin ta sami karfin halin fadin
“Jan inajin fa haihuwace za tayi asibiti ya
kamata mukai ta”maganar da Hannatu tayi ne
yazame masu tuni akan abinda yakamata suyi,
nan da nan kuwa suka kinkimeta zuwa waje a
motar ta suka sakata hannatu ta zauna da ita a
baya yayinda Jan ke tukin motar bakon su Kuma
a gaban motar,
Gudu Jan keyi na fitar hankali tamkar zai tashi
sama burinsa bai wuce ya gansu a asibiti ba a
duba masa Hajiyarsa ba Fadi yake a zuciyar sa
‘shikenan ya banu ya lalace asirin sa yagama
tonuwa asirin boye yafito fili’.
Daya zuciyar sa ke raya masa me zai hana
kawai ya wawashe dukiyar Hajiya ya kara gaba
abinsa, yaje ya dauki yar tsohuwar sa da Hany
dinsa su canza gari, kai suma bar kasar gaba
daya ta yanda babu yanda za ayi a ganinsa.
A hankali yasauke ajiyar zuciya yayin da dayar
zuciyar ta sa ke fadin ‘kai Jan ka kwantar da
hankalin ka kawai tunda ga halin da Hajiyar take
aciki, ba Sai ka gudu ba dafa ta mutu yanzu
dukkan dukiyar ta yazama naka tunda bata alaka
da kowa bare asan tama mutu.
Dan guntun tsaki yaja a hankali yake furta
idan Hajiyata ta mutu ai nima na mutu dan bana
jin zan iya rayuwa ba tare da wannan yar
tsohuwa ba! Gabansa ne yayi mummunar
faduwa daya tuna kalmar ta takarshe, “Jalal
kaine mijin yata Hannatu!!!?”
Ya tabbata baiji da kyau bane saboda ta gaya
masa yaro daya ta haifa kuma ya mutu, sauri
yayi ya kawar da wannan tunanin mara dadi.
A jiyar zuciya mai karfi yasauke har sai da
bakon nan yayi saurin duban sa.
“Hannatu kuwa ta kasa gane a wani yanayi take
ciki, murna takeyi daganin wacce aka ce itace
mahaifiyar ta wacce sam bata amsa matsayin ta
na uwa a gurin taba, domin kuwa a ganinta sam
ba tayi mata adalci ba da yafe ta, ta sallamata a
lokacin da take tsananin bukatar ta bata taba
waiwayar taba koda sau daya ne tsawon
shekarun nan sai yau da Allah yasa suka hadu a
dalilin da ita kanta bata sani ba, wannan wace
irin uwa ce da bata son yar ta data haifa da cikin
ta?” a daya bangaran na zuciyar ta kuwa tana
mamakin abinda yasaka ta shiga wannan halin
dan kawai sunyi ido hudu da mijin auran ta! Shi
dama Sun san juna ne? Kokuwa akwai wani abu
a tsakanin sune? “Hmm Gaskiya tana tsananin
bukatar amso shinta! Shin wa zai amsa mata ne
Jan kokuwa Hajiya wacce ke kwance bisa cinyar
ta. Gabanta ne ya yanke yafadi rass!!! Ganin
jikin Hajiyar ya saki bata motsi, a gigice tace
“kawu!Tafa daina motsi kalla ka gani!! ”
Dasauri yajuyo yana duban fuskar ta, yana
fadin
“Innalillahi…….” Wani mahaukacin burki Jan
yaja motar tashiga tangal tangal Allah dai ya
tsare ta tsaya cak, cikin wani irin sauri tamkar
ya kifa yazagayo ta dayan kofar, jijjiga ta
yafarayi yana fadin
“Hajiya! Hajiya!! Dan Allah karki tafi kitashi
Hajiya!” Dakyar bakon da aka kira da kawu ya
lallashi Jan kafin ya natsu Amman sam yaki
yarda yayi tukin saidai shi kawun yaci gaba da
tukin yayin da Hannatu ta koma gaba shikuma
Jan ya kankame Hajiya a bayan motar.
Sosai kawu yayi gudu da motar har Allah yakai
su asibitin lafiya Jan sai sambatu yake tayi, nan
danan aka gungura Hajiya bisa gadon daukar
marasa lafiya, dakin haihuwa aka nufa da ita kai
tsaye, likitoci biyu mata ne suka rufu akanta
cikin kwarewa da aikin su tsawon wani lokaci
anata abu daya amman har yanzu haihuwa
shuru, Jan kuwa tamkar ya tura kai cikin dakin
haka yake ji, sai faman safa da marwa yake tayi
a tsakanin dakin haihuwar da reception din,
tuni yafice a hayyacinsa harma bai san me yake
fadi ba,
Likitar ce tafito fuskar ta a daure tace masu tana
son ganin su a office dinta, wani irin harara Jan
yasakar mata cikin hargagi yake fadin “dallah
malama ki fadi duk wani abinda zaki fadi basai
daya daga cikin mu yabiki ko ina ba Amman ki
tabbatar bace min zakiyi matata ta mutu ba!!”A
gigice Hannatu tayo kansa, taba fadin “JAN
hauka kakeyi ne? kwakwalwar ka ta tabune
dakake kiran mahaifiya ta da matar ka? Gani
nan fa tsaye gaban ka kake kiran wata da
matarka” cikin rashin damuwa da hayaniyar da
sukeyi a tsakaninsu likitar ta fara magana domin
kuwa ta kule da maganar da Jan yagaya mata.
“dama so nake ingaya maku bazata iya
haihuwa da kanta ba sai anyi mata aiki dan kuwa
mahaifar ta tayi laushi dayawa ta sha haihuwa
fiye da kima wanda hakan yasa bazata iya
haihuwa da kanta ba dan haka kai da kake
ikirarin mijinta ne kazo kasa Hannu.”
ta wuce abinta tabar su nan sake da baki kuka
Hannatu ta fashe dashi da karfi tare da sakin Jan
wanda yarasa awani duniyar yake ciki shima,
Shin abinda ya jiyo ma kunnen sa gaskiya ne?
Da gaske Hajiya mahaifiyar matarsa ce,
Ko Kuma rudun da ya shiga ne yasa kunnuwan
sa sake jin hakan.?
“Da karfi ya juyo yayi gun Hany da ta durkushe
tana wani matsanan chin kuka”
Kukanta ya bayyana masa abinda yaje tunani,
tabbas Mamanta ce,
Tsaya wa yayi kamar an dasashi a gun, komai
nasa baya aiki,
Likita ce ta kara fitowa tana maseefa.
Ganin yanayin da suke ciki yasa tadan sassauta,
komawa tayi tazo da wata takarda Amma ba
Wanda ya iya karba cikinsu,
“Idan fa Baku saka hannu ba zata mutu”
Gaba dayan suka zabura suka yo kan Dr. Da
nufin karbar takardar Jan aka baiwa ya saka
hannu.
Hany ta shiga yanayin da bata San kalarsa ba,
numfashinta ne ya fara chijewa yana yin sama-
sama zuciyar ta tamkar ta fito waje ta rasa gane
me takeji.
Kuka yakeyi tamkar jiniya irin yanda yara
kanana suke yi idan sun kare kuka, sautin
wannan kukan yafi dafa zuciyar mai sauraren sa
fiye da kuka.

Comments

Popular Posts