RUGUNTSUMI PART 13..5/2/2017

Numfashin sane yaji yana neman d’aukewa jin
ta kira wani da bobo, dak’yar yasamu ya daidai
ta natsuwar sa, gaba daya yarinyar ta tafi da
imaninsa, wani irin abu yake ji a zuciyar sa
game da ita.
Ita kuwa cikin natsuwa da taku na hadaddun
mata ta wuce kamar batasan Allah yayi ruwansu
a gun ba, duk da cewa bata kalli gefen su ba
kawai wucewa tayi saboda tasan zasu biyota.
Ahmad ne yarike hannunsa jin kalaman dake
fitowa a bakinta, cak suka ja suka tsaya.
JAN ya k’ara kallonta daga sama zuwa kasa wata
irin tafiya ce takeyi cikin yanga.
bazai iya tantance meye aransa ba game da ita,
ya fara taku zai nufi kanta Ahmad ya riko
hannunsa “ina zuwa JAN?” ya fizge hannun
sannan yace
“gunta mana, sai angwada ake sanin na
kwarai”
Ya fada yana ya gyara rigarsa shi dole babban
yaro sannan ya nufi inda take tafiya.??
Sallama yayi ahankali ta dago idanuwanta don
ganin mai wannan
sanyayyar muryar, da sauri ta kauda idonta ta
mayar kasa da suka hada ido, Yarrrr taji tsigan
jikinta ya tashi don shima kallonta yakeyi ko
kiftawa bayayi, aranta kuwa cewa take ‘ko don
kaga kana da ido masu kashe jijiyan mutum yasa
kake kallona haka, toh karyanka ni sai Bobo na’
a fili kuwa amsa sallamar tayi sannan taci gaba
da tafiya, binta yaci gaba dayi yayinda take sauri
saboda kar ya tsaidata sabida batada lokacinsa
take gani, shikuwa binta yake har ta isa wani
gida ta shige, tana shiga ta rufe gate din,
shikuma ya tsaya yana jira yaga ko akwai wanda
zai fito daga gidan, yafi minti goma a tsaye don
harya juya zai tafi wani tsoho yaleko zai dauki
buta dasauri ya nufe shi “Baba ina wuni? inada
tambaya” tsohon ya kalleshi sama da kasa
sannan yace  “meya faru?” JAN ya gyara
tsayuwarsa sannan yace “Baba akwai wacce ta
shiga ciki yanzunnan, nace inaso nayi sallama da
ita amma ta shige ko zan san sunanta?” Tsohon
ya kalli JAN sama da kasa ganin yadda yake
magana da karfin gwiwanshi sannan yace
“Hannatu kake magana? fara doguwa ko?”
dasauri ya gyada kai sannan yace ” ae ita!
wallahi baba da alheri nazo Hannatu sunanta
kenan” tsohon ya kuma kallonshi ya leka
bayansa yaga ko da wani abu yazo yaga dai da
sayyadansa (kafafu) yazo babu babur balle mota,
saidai dan gayune, a ransa yace irin gayun
yarannan masu bakar karya ba ko kobo.
gashi yarinya masu nemanta babu na kafa don
haka kawai yayi murmushi sannan yariko
kafadan JAN ya janyoshi sannan yace “kaga ita
Hannatu nemanta shine zai baka wahala, yanzu
dai kayi hakuri idan ka samu wata Allah ya baka
ko?” JAN ya kalli tsohon duk da bai gama
fahimtan me yake fada ba ya ce “toh baba!
nagode” ya mayar da hannunsa cikin aljihu
sannan yaci gaba da tafiya don komawa gun
daya baro Ahmad tare da motarsa, cike da
takaicin rashin magana da Hany, duk da cewa
ya kwallafa ransa cewa tabbas yazama dole
agaresa yanemi Hannatu.
Tundaga nesa ya hango Ahmad ya tsura masa
ido yana jiran karasowar sa, d’aure fuska yayi
dan yasan tsiya zai mashi tunda ya tsura mashi
mayun idanuwansa. Aikuwa yana karasowa
Ahmad ya kwashe da dariya harda bugun motar,
dariya yaketa shak’awa tamkar wani sabon
mahaukaci, JAN ya kulu iya kuluwa sai kallonsa
yake yana sake saken abinda zai masa…..

Comments

  1. RUGUNTSUMI PART 13..5/2/2017 http://mubarakadamu.blogspot.com/2017/02/ruguntsumi-part-13522017.html

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular Posts