RUGUNTSUMI PART 20....12/2/2017
Wani bakin ciki ne ya tokareta, bata san
lokacin da ta fizge wayan ba da karfi ta wurgar
akasa, wanda tuni ya fashe a gurin, tana hushi
kaman mayunwacin zaki, domin ji take kaman ta
rufe shi da duka , shi kanshi ya tsorata domin
bacin ran da yagani a fuskanta dazu bai kai na
yanzu ba, jikinshi ya fara rawa kaman wanda
aka kama yana sata.
“Jalal ni kake cewa zaka barni koda zaka
mutu?”
Ta fada da wata irin raunatacciyar murya mai
ban tausayi, ta dago kai ta kalleshi,
“Maimaita abunda kace” ya kalleta idonshi
arazane ya sunkuyar da kai tare da cewa
“fada kawai nake yi, wata ce da naje Nasarawa
taji labarinki take tsorata ni akan zata fadawa
Mamasko abunda ke faruwa”
Duk da yasan maganan shi tayi kama da na
rainin hankali amma danne zuciyarsa yayi
kaman dagaske yake nufi sannan cikin wayo
irinta mayaudaran maza yace “taji labarinki da
kuma irin zaman da mukeyi, budurwa ta ce ada
amma mun rabu wallahi, shine fa take cewa na
rabu dake ko ta fadawa Mamasko, kinga kuma
Mamasko bata da ishashen lafiya kar ta tayar
mata da hankali tazo ta hanani tahowa nan
dinma, shine yanzu nake lallabinta inaso nasa
acikin abokai na ko kudi sukai mata domin su
toshe bakinta” duk da radadin da take ji da
haushinshi da takeji ta tsinci kanta da amincewa
da maganarsa, ta gamsu sosai anan taja wani
numfashi wanda shi kanshi sai da yayi mamaki
sannan tace
“Jalal miye gaskiyar zancen da wannan
yarinyar ta fada dazu? Pls kada ka boyemin
komai dan Allah”
Ya gyara tsayuwarsa sannan yace,
“Hafsa tsohuwar budurwatace shekara kusan
shida da suka wuce,”
Nandai ya bata labarin Hafsaa daga farko har
karshe, Hajiya ta gamsu da bayanin sa,
“kayi hakuri don Allah, amma ka daina yimin
haka, wata ran zan iya hadiyan rai na mutu, ina
tsananin sonka fiye da duk wani abu dana
mallaka ,ka rufa mini asiri don girman Allah ka
taimakeni JAN”
Yadda take riko hannunshi take rokonshi yayi
bala’in tsoratashi har ta janyoshi suka shiga daki
aka fara aikin masha’a waiyazzubillah muna
neman tsari.
Duk da cewa rabin hankalinshi yana kan
Wayan da ta fasa, yana tunanin Hany dinsa,
domin kuwa yasan zata yita nemanshi, sannan
zata iya shiga tashin hankali tayi tunanin ko
wani abu ya sameshi, don haka rabin tunaninsa
yana kan fita siyan sabon waya, amma Hajiya
kam taki barinsa sai karfe goma na dare
tabarshi ya fita, aikuwa yana wanka yace mata
zaije dominos ne yasiyo pizza anan wuse2, bata
yi musu ba ganin babu wani nisa sosai, yana fita
bai tsaya bata lokaci ba yaje neman waya, duk
da bai gama sanin kan gari ba shine gam village,
shine bannex bai samu wayan ba, don haka
kawai yafara bin titi ko zai ga shagon waya,
ahaka yasamo wani ba tare da duba sunan
shagon ba, yashige yasiyo sabuwar waya da
sabuwar sim sai dai babu masu register, nan dai
ya tuna akwai wata tsohuwar sim da yakeda,
donhaka dasauri ya binciko motan ya dauko ya
jonata acaji ya sayi kati sannan ya kunna dama
ya rike numban Hany da sauri yakira, muryanta
a dishe ta dauki wayan, alamun taci kuka.
“Babyna me ya sameki?” jin muryarsa yasa
takara fashewa da kukan, tuni ya kara rudewa
yafara bata hakuri, duk da bai san dalilin kukan
ba, amma yasan bai wuce shagwabar da ta
sabayi masa bane, saboda kusan kullum Hany
sai ta masa kuka wai ita ta matsu yazo suyi aure.
Ya isa gida Hajiya bata gane komai ba, saboda
haka kai tsaye daki ya shiga, ya boye wayar sa,
Hajiyace ta shigo dakin kamar an korota, shi
kansa Jan saida ya firgita,
Cikin tsananin kulawa da natsuwa tace.
“Jalal”
Sai kuma tayi shiru, dago ido yayi ya kalleta,
matsowa tayi kusa dashi ta kama hannayensa
duka biyu ta rike,
“Jalal so nake muyi Aure.”

RUGUNTSUMI PART 20....12/2/2017 http://mubarakadamu.blogspot.com/2017/02/ruguntsumi-part-201222017.html
ReplyDelete