RUGUNTSUMI PART 21...13/2/17
Zuciyarsa ce tayi wani irin bugawa a rikice ya
nanata kalmar ta takarshe “Aure!!? Kara damke
hannuwansa tayi cikin nata tace “eh! Jalal aure
nakeso muyi, ina ganin wannan hanyar ce kawai
zaisa in mallake ka yanda nakeso hankalina zaifi
kwanciya zanfi samun natsuwa! “wani irin kallo
yakeyi mata ido cikin ido, kai tsaye yashiga
girgiza kansa alamar zancan ta bai shige shiba,
ido ta tsare shi dashi tana fadin “JAN! Kalli cikin
ido na kace baka sona bazaka iya auran tsohuwa
ba sai intabbatar dacewa lallai kai…… ” Katseta
yayi dasauri ta hanyar saka bakin sa cikin nata
yana mai girgiza mata kai, hawaye ne yafara
gudu bisa fuskar ta dasauri ta ture sa daga
jikinta cikin rawar murya tace “Jan bazaka iya
aure na ba ko?” cikin wani irin salo irin ta
mazan bariki yashiga yi mata dadin baki hade da
kalamai masu dadi wayanda zasusa hankalin ta
ya kwanta, daga k’arshe ya amince akan cewa
zai aure ta,
****************************************
Shagalin bikin JAN akeyi babu kama hannun
yaro, biki ne na karya da kece raini naira tayi
kuka sosai awannan shagalin biki Ango yadaukar
ma kansa k’arya inda ita ma amarya ta nuna
masa tafisa iyawa, Amarya Hannatu tayi kyau
har ta gaji iya haduwa ta hadu ba karya, Ango
Jan sai shiga kala kala akeyi ana sakewa sai kace
wani ma’aikacin gwamnati, kowani mai arziki,
party har kala biyar akayi yabarwa samari yan
kwalisa abin fadi cikin unguwa, an daura auran
da misalin k’arfe biyu da rabi ranar juma’a
bayan an sakko sallar juma’a, daurin auran
yasamu halartar dubbannin Jama’a, bakin ango
sam yakasa rufuwa sai kace gonar auduga.
Amarya ta shige gidan ta wanda musamman Jan
yakashe makudan kudade wajan gina shi( kudin
hajiya da ta bashi daman amfani dashi) ,gida ne
madaidaici nagani na fadi, ya hadu yakuma
tsaru iya tsaruwa sai dau muce Allah yabada
zaman Lafiya!
**********************
Sati biyu Jan yayi a suna gurzar amarci shida
amaryar sa, ji yake tamkar karya koma abuja
amma idan yatuna hajiyar sa a bangare daya
gabansa har faduwa yakeyi yana tsananin tsoron
hajiya tasan abinda ya aikata domin Kuwa yana
ganin yaci amanar hajiya ya munafurce ta, har
a zuciyar sa yanajin babu dadi abinda yai mata
saidai babu yanda zaiyi ne kaddara tariga fata!
Acewar sa haduwar sa da Hannatu hadi ne daga
indallahi! yasan ko a mafarki auren hajiya ba
nashi bane, zai ci kudinta dai sannan ya biya
bukatunsa.

RUGUNTSUMI PART 21...13/2/17 http://mubarakadamu.blogspot.com/2017/02/ruguntsumi-part-2113217.html
ReplyDelete